ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, November 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shekaru 75 Masu Albarka

by CGTN Hausa and Sulaiman
1 year ago
Albarka

Gobe ke bikin cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, a wadannan shekaru 75 da suka gabata, karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS), al’ummar Sinawa sun yi nasarar juyin juya halin demokradiyya, kuma sun kai matsayin da za su iya tantance makomarsu. Sai dai kuma a wannan shekarar, Dean Acheson, sakataren harkokin wajen Amurka na lokacin, a kokarin yin bayani kan musabbabin juyin juya halin kasar Sin, ta hanyar nazarin yanayin tattalin arziki da akidar kasar Sin, ya danganta juyin juya halin da abubuwa biyu wato “yawan jama’a” da “kwararar sabbin ra’ayoyi daga yamma”. Canki cankar Acheson na “yawan jama’a” ba ya da tushe. Saboda a tarihi, duk inda aka yi zalunci da cin zarafi, to dole a fuskanci turjiya, ko da yake siffofi da hanyoyin wannan turjiya na iya bambanta amma wannan ita ce mahangar tarihi.

Juyin juya halin dimokradiyya ta kasar Sin ya ruguje tsohon tsari da samar da wata sabuwar al’umma da za ta mallaki kasarta wadda za ta tsaya da kafafunta kuma da mutunci, kuma ita ce jigon ci gaban kasar. Kamar yadda gwamnatin kasar Sin ta sha nanata cewa, dan Adam ya fi komai daraja a duniya. Kuma karkashin jagorancin jam’iyyar JKS, muddin akwai mutane, za a iya samar da kowane irin abin al’ajabi.

ADVERTISEMENT
  • ICPC Ta Ƙulla Yarjejeniyar Haɗin Gwuiwa da Wata Hukuma A London
  • Me Ya Sa Sin Da Sauran Kasashen Duniya Ke Cin Moriya Tare a Cikin Shekaru 75 Da Suka Gabata Tun Kafuwar Sabuwar Kasar Sin?

Tun daga shekarar 1949, jam’iyyar JKS ta jagoranci al’ummar kasar wajen gaggauta farfado da tattalin arzikin kasa, wanda tsohuwar gwamnatin ta yi wa illa sosai. Duk da kasancewarta kasa mai girma da talauci mai yawan jama’a, kasar Sin ta samu ci gaba sosai wajen bin tsarin gurguzu, inda ta fara aiwatar da ayyukan gina kasar bisa tsarin gurguzu, wadanda suka shafi aikin gona na zamani, da masana’antu, da tsaron kasa, da kimiyya da fasaha.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 

Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

Tun kafin kaddamar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga waje a shekarar 1978, kasar Sin ta yi nasarar kafa tsarin tattalin arzikin masana’antu da na kasa mai cin gashin kansa a hankali. Kuma ta ci gaba da zurfafa gyare-gyare a fannin tattalin arziki, yayin da take ci gaba da yin gyare-gyare a harkokin mulki, da al’adu, da al’umma, da dai sauransu bisa tsarin gurguzu. A ko da yaushe ci gaban kasar Sin ya kasance yana da alaka da duniya, kamar yadda ci gaban duniya ke bukatar kasar Sin. Kasar Sin ta yi matukar tasiri a tarihin ci gaban bil Adama. Kuma ta kasance muhimmin karfi na ciyar da dan Adam gaba. (Mohammed Yahaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 
Daga Birnin Sin

Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 

November 17, 2025
Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

November 17, 2025
An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing
Daga Birnin Sin

An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing

November 17, 2025
Next Post
Amurka Ce Za Ta Yi Fama Da Mummunan Tasirin Tallafin Da Take Bayarwa Ga Neman ‘Yancin Taiwan

Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Sauka A Jihohin Arewa Maso Gabas

Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Sauka A Jihohin Arewa Maso Gabas

November 17, 2025
An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing

An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing

November 17, 2025
NBS

Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ta Ragu Zuwa Kashi 16.065%

November 17, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO

Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO

November 17, 2025
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

November 17, 2025
Kudaden Kasafin Kudin Sin Sun Karu Da Kashi 0.8 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

Kudaden Kasafin Kudin Sin Sun Karu Da Kashi 0.8 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

November 17, 2025
Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi

Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi

November 17, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejeniyoyin Cinikayya Na Biliyoyin Kudi Yayin Baje Kolin CHTF Na Kasar Sin

An Sanya Hannu Kan Yarjejeniyoyin Cinikayya Na Biliyoyin Kudi Yayin Baje Kolin CHTF Na Kasar Sin

November 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.