Yayin da tutoci suka rika kadawa, kade-kade na tsuma maza suka rika tashi, kusan ko ina ya cika da batun tarihi a titunan birnin Beijing, ba sai an fada ba sakon ya fito fili karara, wato jama’ar kasar Sin na tunawa da samun nasararsu a kan kare martabar kasa daga zaluncin mamayar dakarun Japanawa.
Yau Laraba, 3 ga watan Satumba, rana ce ta cika shekaru 80 da samun wani muhimmin lokaci a tarihin zamani da ya kunshi manyan abubuwa biyu, na farko nasarar jama’ar kasar Sin a kan zaluncin Japanawa, da kuma babbar nasarar da sojojin kawance suka samu a yaki da mulkin danniya a duniya wanda aka fi sani da Yakin Duniya Na Biyu.
- Kungiyar Kare Shirye-shiryen Tinubu Ta Nemi A Dakatar Da Shugaban Kamfanin NNPCL
- NAFDAC Ta Gano Wasu Jabun Allurai A Kasuwanni, Ta Gargaɗi Jama’a Kan Amfani Da Su
Gagarumin bikin ranar da aka yi yau a kasar Sin ba wai kawai na tunawa da nasarar soja ba ne, girmamawa ce ga tsayin daka, sadaukarwa, da hadin kan al’ummar da ta yi fama da tashe-tashen hankula na tsawon shekaru 14. Tun daga abin da ya faru a ranar 18 ga Satumba a shekarar 1931 (na kaddamar da hare-hare) zuwa mika wuyar kasar Japan a shekarar 1945, kasar Sin ta yi gwagwarmayar tsira da mutuncinta daga mamayar zalunci har ta kai ga asarar rayukan sojoji da fararen hula fiye da miliyan 35. Kuma duk da shiga cikin tsananin wahalhalu da ba za a iya misaltawa ba, jama’ar kasar Sin sun tsaya tsayin daka, tare da ba da gudummawa sosai ga fatattakar ‘yan mulkin danniya a duniya.
Gadon tsayin dakar da jama’ar kasar Sin suka yi shi ne ya zama ruhin kasar, ya kuma ba da gudunmawa ga haifar da sabon tsari na duniya a karkashin Majalisar Dinkin Duniya, tare da sadaukar da kai ga zaman lafiya a tsakanin al’ummomin duniya. Sai dai kuma, a yayin da tashe-tashen hankula a duniya ke kara ta’azzara a zamanin nan kuma masu ba da labarin abin da ya faru suka fara gurbata hakikanin tarihi, rawar da kasar Sin ke takawa wajen kare gaskiyar lamarin na da matukar muhimmanci.
Jawabin da shugaba Xi Jinping ya yi a taron Tianjin na Kungiyar Hadin Gwiwar Shanghai (SCO), ya sake jaddada aniyar kasar Sin wajen raya mu’amala da bangarori daban daban, da daidaiton ‘yancin kasashe, da hadin gwiwar duniya baki daya. Gabatar da shawarar Tsarin Shugabancin Duniya (GGI) ta nuna sabon kokari na kiyaye kyawawan ka’idojin da aka kafa bayan yakin duniya na biyu domin ci gaban kasa da kasa.
Kazalika, wannan biki na tunawa da nasarar fatattakar zalunci yana tunatar da mu mahimmancin waiwaye a kan tarihi. Fina-finai da aka yi game da hakan kamar “Dead to Rights”, da bikin nune-nunen a sassan yankin Macao, da faretin soja a birnin Beijing, hidindimu ne na sake duba tarihi, da sadaukarwar al’ummomin da suka gabata domin ci gaba da zaburar da na yanzu da wadanda za su zo gaba.
Birnin Beijing ya cika da annashuwa da alfahari yayin da dandalin Tian’anmen ya shaida gagarumin faretin soji domin bikin na yau. An yi gaisuwar ban-girma ta hanyar harba bindigogi 80 a sassan babban birnin domin karrama mazan jiya da suka kwanta dama da kuma wadanda suke raye. Sojoji sun yi tattaki cikin tsari mai kyau, jiragen sama sun yi fenti mai launin ja da zinariya a sararin sama, kuma tsoffin sojoji da suka halarci bikin sun kasance a matsayin shaida na jajircewa.
Shagulgulan al’adu da shirye-shiryen gidajen rediyo da talabijin da aka watsa a sassan kasar har ma da duniya baki daya sun kara raya ruhin tunawa da wannan nasara a cikin gidaje da zukatan jama’a a fadin kasar da sauran abokai na kasa da kasa. Yanayin yau a kasar Sin ya kasance na biki mai matukar armashi da ke kara girman kishin kasa tare da girmamawa ga sadaukarwar da aka yi shekaru 80 da suka gabata.
Darussan wannan tarihi a bayyane suke, wato hadin kai wajen fuskantar zalunci da kuma kiyaye mutunci domin tabbatar da adalci a doron kasa kuma tabbas, kasar Sin ta nuna gado mai kyau ta wannan fuska. Don haka, ya kamata wannan rana ta zama ba lokacin tunani ne kawai a kan nasarar da aka samu ba, amma a kan abin da ya zama wajibi a kiyaye shi. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp