Lokacin da Rt. Hon. Sheriff Oboreɓwori ya karɓi rantsuwar kama aiki a matsayin Gwamnan Jihar Delta a ranar 29 ga Mayun 2023, bai zo da wasa ba.
Ya zo da taswirar ta hanyar ajadarsa mai suna, ‘MORE Agenda’, wadda ke ɗauke da falsafar ci gaba mai matuƙar ma’ana, bai wa kowa dama, gyare-gyare, gaskiya da Inganta zaman lafiya da tsaro.
- Sojoji Sun Kama Mutane 69 Masu Fasa Bututun Mai A Yankin Neja-Delta
- Kotu A Kano Ta Tsare Wani Mai Gidan Marayu Bisa Zargin Satar Yara Da Safararsu Zuwa Delta
Bayan shekaru biyu, Jihar Delta ta canza sakamakon ayyukan alhairin da ya aiwatar a bayyane. Tun daga kan tituna da gadar sama zuwa makarantu da asibitoci daga kula da tsarin kasafin kuɗi zuwa ci gaban kasuwancin jama’a, Gwamna Oboreɓwori ya nuna cewa; idan aka tsara mulki, aka kuma aiwatar da shi cikin tausayawa, zai iya canza rayuwar al’umma.
Daga Majalisa Zuwa Jagoranci
An haife shi a ranar 19 ga Yunin 1963, Sheriff Oboreɓwori ba baƙo ba ne wajen hidimta wa jama’a.
Kafin ya zama gwamna, ya kasance Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Delta, inda ya yi ƙaurin suna wajen yin adalci, kwanciyar hankali da kuma zurfin fahimtar shugabanci.
Wannan gogewa ta aikin doka, ta zama ginshiƙin nasararsa na gudanarwa. Kazalika,ya ba shi damar daidaita hangen nesa da tuntuɓa tare da yin taka- tsan-tsan wajen aiwatar da ayyukansa.
Ajandarsa Ta “MORE Agenda”
Ajandarsa ta ayyukan da yake ƙuzun aiwatarwa, ƙarƙashin “MORE Agenda”, Gwamna Oboreɓwori, ba wai kawai taken ba ne; tsari ne na aiki wanda ya ƙunshi kowane ɓangare na ayyukan da son aiwatarwa ƙarƙashin mulkinsa
A Ƙarƙashin Jagorancinsa:
An kammala ayyukan tituna sama da 513 da suka shafe kusan kilomita 1,500, ban da kuma waɗanda ake kan ci gaba da gudanarwa a halin yanzu.
Tashar jiragen sama kamar ta ‘PTI Junction, Enerhen, shataletalen DSC, da gadar sama ta Effurun, sun yi matuƙar sake fasalin biranen jihar.
Waɗannan ayyuka, musamman waɗanda aka rarraba a dukkanin gundumomin majalisar dattawa guda uku, suna nuna manufar ci gaban da aka samu tare da nuna cewa; babu wata al’umma da aka bari a baya.
Amma hangen nesansa, ya wuce kwalta da gadoji kaɗai. Ya game mutane, ba kawai wurare ba; gina amana, ba kawai ababen more rayuwa ba.
“Wajibi ne ci gaba ya zama wani abu da ya shafi kowa da kowa, a ko’ina cikin Jihar Delta,”.
Ilimi A Matsayin Tushen Ci Gaba
Ganin cewa, ilimi shi ne tushen ci gaba, gwamnatin Oboreɓwori ta sanya hannun jari a makarantu da ɓangarorin horarwa.
Kama daga sabunta tubalan ajujuwa, ɗakunan gwaje-gwaje da cibiyoyin ICT zuwa ɗaukar sabbin ma’aikatan koyarwa da na sauran ma’aikata sama da 5,500, sannan ana sake fasalin sashen ilimi na Jihar Delta, domin nan gaba.
Sama da ɗalibai 60,000 ne aka raba wa tallafin kuɗi sama da Naira biliyan 1, yayin da aka inganta kwalejojin fasaha da cibiyoyin koyar da sana’o’i, domin bai wa matasa sana’o’in dogaro da kawunansu.
Saƙon a bayyane yake cewa: a cikin Oboreɓwori ta Jihar Delta, kada a bar yara a baya.
Kula da kiwon lafiya da kwanciyar hankali,
Tsarin kiwon lafiya na Jihar Delta ya shaida juyin- juya-halin da aka samu a ƙarƙashin kulawarsa.
Kazalika, cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko a dukkanin ƙananan hukumomi 25, ana kan gyara su tare da sabunta su da kuma kayan aiki.
Asibitin Ƙwararru na Asaba a halin yanzu, yana alfahari da kayan aikin binciken da samu irin wanda duniya ke tunƙaho da su, gami da MRI, CT da sassan ɓangaren nan wankin ƙoda.
“Wannan wani babban ci gaba ne a ƙudurinmu na samar da kiwon lafiya na duniya ga al’ummar Jihar Delta,” in ji Dakta Peace Ighosewe, babban daraktan kula da lafiya na asibitin.
Haka zalika, an faɗaɗa ɗaukar nauyin inshorar lafiya, sannan kuma Shirin Tallafin Lafiya na Jihar Delta a halin yanzu, ya tallafa wa dubunnan ‘yan ƙasa masu rauni waɗanda a baya ba su da damar samun kulawa ta yau da kullum.
Ƙarfafawa Ta Hanyar Samar Da Damammaki
Dangane da alƙawarinsa na “Samar da damammaki ga kowa da kowa”, gwamnatin Gwamna Oboreɓwori, ta yi yunƙurin ƙarfafa matasa da mata ta hanyar taimaka musu.
Sama da ’yan asalin Jihar Delta 250,000 ne suka ci gajiyar ayyukan jin daɗin jama’a da ake yi wa manoma, masu sana’a, mata da kuma nakasassu.
A ɓangaren aikin noma, yana tallafa da kayan aikin gona, samar da bashi, domin samun damar dogaro da kai.
Matasan manoma a halin yanzu, suna aiki a gungu na haɗin gwiwa tare da samar da abinci da kuma ayyukan yi a faɗin jihar.
Ladabin Tafiyar Da Harkokin Kuɗi Da Zaman Lafiya Da Kuma Kyakkyawan Mulki
Jagorancin Gwamna Oboreɓwori, ya kuma sake fasalin kuɗin gwamnati. Inda ya ɓullo da tsarin bin diddigin kasafin kuɗi a zamanance, ya kuma daidaita ma’aikatan gwamnati tare da aiwatar da sabon tsarin nan na mafi ƙarancin albashi na N77,500 ga ma’aikata, tana ɗaya daga cikin Jihohin Nijeriya na farko da suka fara yin hakan.
Haka nan, ta hanyar ba da fifiko ga gaskiya da riƙon amana, ya kawar da basussukan fansho da aka daɗe ana bin su, ta hanyar samar da Naira biliyan 40 da tsarin biyan albashi a zamanance, don kawar da ma’aikatan bogi.
Waɗannan gyare-gyare, sun ƙara wa ma’aikata ƙwarin gwiwa, sannan kuma sun sa Jihar Delta yin ƙaurin suna wajen sanin ilimin tafiyar da harkokin kuɗi.
A al’amuran tsaro da kwanciyar hankali kuwa, ya kasance wanda ya gina gada, ta hanyar tattaunawa akai-akai tare da ƙungiyoyin matasa, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma, babu shakka ya wanzar da zaman lafiya a jihar da ta jima tana fama da ƙalubale.
Tallafin da gwamnatinsa ke bai wa jami’an tsaro, ya sake ƙarfafa jami’an tsaron tare da sanya Jihar Delta a matsayin guda daga cikin jihohin da suka fi tsaro a Kudu maso Kudu.
Sake Faɗaɗa Jihar Delta
Gwamna Oboreɓwori, ba cikin gida kaɗai ya tsaya ba, aikin zuba jarin da ya yi a Ƙasar Sin a baya-bayan nan ya jaddada burinsa na sanya Jihar Delta cikin taswirar tattalin arziƙin duniya.
Ko shakka bab, wannan tafiya ta mayar da hankali ne a kan haɗin gwiwa a fannin makamashi, fasaha, sauran ababen more rayuwa, musamman wajen bayar da damar iskar gas, don tsabtace makamashi da faɗaɗa masana’antu a jihar ta Delta.
Haka zalika, ya kuma sabunta tsarin shari’a tare da sabbin gine-ginen manyan kotuna da kyautata jin daɗin alƙalai, da sarrafa shari’o’i ta hanyar amfani da kayan zamani, duk don neman ingantaccen tsari na adalci.
Yin Suna Da Kuma Barin Tarihi
Ƙoƙarin da ya yi a cikin shekaru biyu kacal, yasa Gwamna Oboreɓwori ya yi suna:
Ya samu lambar yabo a matsayin;
Gwamnan Jihar a Silɓerbird (2023)
Sai Thisday/Tashi Gwamnan Shekara (2024)
Gwamnan Ɓanguard na Shekara (Infrastructure) 2024.











