Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya yaba wa jami’ar Bayero ta Kano (BUK) bisa yadda ta ke samar da ingantaccen ilimi ga ‘yan Nijeriya tsawon shekaru.
Shettima ya yi wannan yabon ne a lokacin da yake bude bikin taron ajin karatun BUK na shekarar 2004 a harabar jami’ar a ranar Asabar, 7 ga watan Disambar 2024.
Ya kuma yaba wa jami’ar kan yadda take bai wa daliban da suka cancanta guraben karatu ba tare da la’akari da asalinsu ba a fadin kasar nan.