Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jinjinawa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa kafa tare da jagorantar Majalisar Kwarewa ta farko (Pioneering State Skills Council) a matakin jiha a Nijeriya, yana mai bayyana wannan mataki a matsayin ci gaba mai matuƙar muhimmanci tare da ƙarfafa sauran jihohi su yi koyi da Kaduna.
Da yake jawabi a taron karo na bakwai na Majalisar Ƙasa kan Kwarewa (NCS) a ranar Talata a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja, Mataimakin Shugaban Ƙasa ya ce juyin juya halin kwarewa shi ne ginshikin yarjejeniyar gwamnatin Tinubu da ‘yan Nijeriya, kuma muhimmin mataki ne wajen cika alƙawarin bunƙasa jari-hujjar ɗan adam.
Ya yaba da misalin da Jihar Kaduna ta bayar, yana mai jaddada cewa jagorancin Gwamna Uba Sani da kuma shigar fiye da dalibai 30,000 cikin Cibiyar Horar da Sana’o’i da Kwarewa ta Kaduna na nuna sahihin kudurin samar da ayyukan yi da bunkasa kwarewar matasa.
Haka zalika, Ministan Ilimi, Dakta Olatunji Alausa , shi ma ya jinjinawa rawar da Gwamna Sani ya taka wajen sauƙaƙa bikin kaddamar da Cibiyar Horar da Sana’o’i da Kwarewa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gudanar, yana mai cewa yanzu haka ana sake fasalin makarantun fasaha na ƙasa baki ɗaya domin su mai da hankali kacokan kan darussa masu amfani da tasiri.
Shettima ya bukaci mambobin NCS da su hada kai bayan wani tsari guda na juyin-juya halin Nijeriya, yana mai gargadin cewa “ba za mu iya gina ma’aikata da za su yi shiri a nan gaba kan tushen rarraba.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp