A ranar 7 ga Agustan nan, sabon tsarin harajin da gwamnatin Amurka ta kira da “daidaitaccen haraji” ya fara aiki, wanda ke nuna kara fadadar manufar kare kasuwa. Hakan bai wai tattalin arzikin duniya kadai zai yi wa tasiri ba, har ma zai jawo mummunan sakamako ga Amurka ita kanta.
Farfesa Wang Xiaosong daga kwalejin tattalin arziki na Jami’ar Renmin ta Sin ya bayyana cewa, a cikin wannan yanayi, gwamnatin Amurka ta tilasta aiwatar da wannan “daidaitaccen haraji” ne domin ta zama damar shawarwari a hada-hadar cinikinta, ta yadda za ta tilasta wa abokan cinikinta ba ta karin fa’idodi. Haka kuma, wannan shiri ne da zai yi fa’ida a lokacin zaben tsakiyar wa’adin gwamnatin, da fatan samun karin kuri’u.
- Xi Ya Bukaci A Yi Dukkan Mai Yiwuwa Wajen Gudanar Da Ayyukan Bincike Da Ceto Bayan Aukuwar Ambaliya A Lardin Gansu
- Sai Ƴan Siyasa Sun Haɗa Kansu Sannan Za Su Iya Tunkarar APC A 2027 – Lukman
Tasirin munanan manufofin harajin yana bayyanawa cikin sauri. Cibiyoyin kasa da kasa da dama sun nuna cewa, alamun kwanan nan sun nuna cewa tattalin arzikin Amurka ya hau “siradin koma baya”.
Cin zarafin Amurka ta hanyar haraji ya kuma lalata amincinta tsakanin sassan kasa da kasa. A halin yanzu, fannin shigar da kayayyaki na Amurka ya yi kasa zuwa kashi 13% kacal a kasuwannin duniya.
Har ila yau, a jiya Alhamis 7 ga wata, bayanai sun nuna cewa, a cikin watanni bakwai na farkon shekarar nan, cinikayyar kayayyaki ta Sin ta ci gaba da nuna kyakkyawan ci gaba, inda ta samu karuwa tsakaninta da kasashe membobin kungiyar ASEAN, da Tarayyar Turai, da Afirka, da Asiya ta Tsakiya, wanda ke nuna karfin juriya da kuzari. Hakan ya kuma tabbatar da cewa, cin zarafi ta hanyar haraji ba zai haifar da alfanu na dogon lokaci ba, maimakon haka, budadden tsarin hadin gwiwa ne kadai zai samar da riba ga kowa.
A cikin shekarun 1930, Amurka ta kara haraji kan kayayyaki sama da dubu biyu na duniya, wanda ya haifar da martanin kasashen waje, da ya kai ga kasar Amurka ta shiga babban koma bayan tattalin arziki. Da wannan misali na tarihi, ya kamata ‘yan siyasar Amurka su koyi darasi. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp