Kawo yanzu za’a iya cewa kallo ya koma sama domin ganin halin da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars zata tsinci kanta bayan da gwamnatin Kano ta samar da shugabancin gudanarwar kungiyar.
Gwamnatin jihar Kano ta nada shugabannin riko na Kano Pillars da za su ja ragamar kungiyar kuma Babangida Little ne zai ja ragamar shugabancin Pillars din da taimakon mambobi 12, don mayar da kungiyar gasar Firimiya ta kasa.
Pillars wadda ake yi wa taken “Sai Masu Gida” na buga karamar gasar kwallon kafa ta Najeriya, bayan faduwar ta daga Firimiya a bara sakamakon rashin tabuka abin arziki a kakar data gabata.
Tuni aka gabatar da shugabannin, kuma sun karbi ragamar aiki da nufin ciyar da kungiyar gaba kuma gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa a shirye take wajen ganin an dawo da kungiyar matakin da aka santa a baya.
Jerin mambobin da za su ja ragamar Kano Pillars.
1. Babangida Little, Chairman
2. Garba Umar, Member
3. Naziru Aminu Abubakar, member
4. Bashir Chilla, member
5. Ali Nayara Mai Samba, member
6. Shuaibu Ibrahim Doguwa, member
7. Rabiu Pele, member
8. Muhammed Danjuma, member
9. Sabo Chokalinka, member
10. Abba Haruna (Dala FM), member
11. Engr. Usman Kofar Na’isa
12. Yakubu Pele, member
13. Comrade Sani Ibrahim Coach, Secretary
Kano Pillars tana buga gasar Super Eight, wadda za ta ba ta damar samun gurbin komawa babbar gasar firimiya ta kasa kuma ana ganin kungiyar zata iya samun tikitin komawa babbar gasar.
An kafa kungiyar Kano Pillars ne a shekarar 1990, kuma ta lashe Firimiya guda hudu, sannan ta zo ta biyu a kakar wasa ta 2009 zuwa 2010, ta kuma dauki FA Cup biyu da kuma Nigerian super cup a 2008.