Kungiyar kwallon kafa ta Liberpool tana fuskantar kakar wasa mai wahala cikin shekaru sama da bakwai, sakamakon rashin nasarar da kungiyar ta yi a hannun kungiyar kwallon kafa ta Leeds United a satin da ya gabata.
Kawo yanzu dai, Liberpool tana mataki na tara a kan teburin gasar Premier League da maki 16, bayan buga wasanni 12 a gasar Ingila ta bana, kuma yanzu Liberpool ta ci wasanni hudu da canjaras hudu aka doke ta a karawa hudu, bayan da wasa biyu ta yi rashin nasara a bara da ta yi ta biyu a gasar.
- Tsegunta Barazanar Tsaro Daga Ofishin Jakadancin Amurka: Wa Abin Zai Amfanar?
- Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Samar Da Fa’ida A Zahiri Ga Jama’ar Afirka
A ranar Asabar Leeds United ta doke Liberpool da ci 2-1 a filin wasa na Anfield a wasan mako na 14 a Premier League, kuma karon farko da aka ci kungiyar a filin wasanta na Anfield tun bayan wasa 29 a jere ba a doke ta ba, rabon da ta yi rashin nasara tun 1-0 da Fulham ta yi a Maris din shekara ta 2021.
Cikin wasanni 29 da ta buga a Anfield ba tare da rashin nasara ba a jere ta ci 22 da yin canjaras bakwai. Liberpool ta yi rashin nasara a wasa biyu a jere kenan, bayan da tun farko Nottingham Forest ta yi nasara da ci 1-0.
Rashin nasara da Liberpool ta yi a Anfield shi ne karon farko tare da mai tsaron baya Birgil ban Dijk a cikin fili, wanda ya yi wasanni 70 a gida ba a doke kungiyar ba, sannan Liberpool za ta buga wasa daya a Premier League kafin a je gasar kofin duniya, shi ne wanda za ta karbi bakuncin Southampton ranar 12 ga watan Nuwamba.
Sai dai lokacin da Liberpool za ta dan sarara har sai bayan gasar kofin duniya, watakila ta kamo bakin zaren, amma kuma me ya sa Liberpool ba ta kokari a bana duk da cefanen da ta yi bayan da ta kare a mataki na biyu a bara da Manchester City ta lashe kofin?
Tun a farko, wasu na cewa duk inda Jurgen Kloop ya yi shekara bakwai a kungiya ya kan ci karo da kalubale a shekara ta takwas, saboda wasu na cewa salon wasa iri daya yake yi shi ya sa idan ya yi shekara bakwai kowa ke gane dabararsa a fagen horar da kwallo.
Haka ya faru a Mainz da Borussia Dortmund da ya yi kaka bakwai a kowacce kungiyar, amma ya kasa kai bantensa a shekara ta takwas kuma ana ganin cewa yawan rauni da ‘yan wasan Liberpool ke yi na daya daga cikin abin da ya sa kungiyar ke fuskantar koma-baya.
‘Yan wasan kungiyar da ke jiyya kawo yanzu sun hada da Thiago Alcantara da Luis Diaz da Diogo Jota da Ibrahima Konate da Joel Matip da Arthur Melo kuma dukkaninsu suna daya daga cikin ‘yan wasan da ke taimaka wa kungiyar.
Sannan a wannan kakar dan wasa Mohamed Salah baya cin kwallo kamar yadda ya kamata, domin kafin wasa da Leeds United kwallo uku ya zura a raga mafi karanci, wanda a Oktoban ya kan ci biyar.
Haka kuma ana hasashen cewar wasu ‘yan kwallon Liberpool shekarunsu sun ja, ya kamata ta kara daukar wasu masu jini a jika ta kara sirkawa idan har tana son ta ci gaba da jan zarenta irin na baya.
Sannan wasu suna ganin tafiyar dan wasa Sadio Mane zuwa kungiyar Bayern Munich a bana ya taba Liberpool, wadda ta dauko Darwin Nunez, wanda ya maye gurbin dan kwallon tawagar Senegal din.
Nunez ya ci kwallo hudu a Premier League ta bana an kuma yi masa jan kati a kakar bana, to sai dai kuma Liberpool na kokari a Champions League, bayan da ta samu gurbin shiga wasannin gaba na kungiyoyi 16.
A ranar Lahadin da ta gabata, Liberpool za ta fafata da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham a gasar firimiya, wasan da kungiyar take bukatar lashewa idan har tana fatan ganin ta ci gaba da neman kammala gasar ta Firimiya a mataki na hudun farko.