A yau Talata ne sakatariyar baitulmalin Amurka Janet Yellen ke kammala ziyararta a kasar Sin. Kuma da yammacin jiya Litinin, jami’ai masu ruwa da tsaki daga ma’aikatar kudi ta Sin sun yi karin haske game da ziyarar, inda suka tabo wasu batutuwa da Sin da Amurka suka amince da su.
Daga cikin batutuwan da suka ja hankalina akwai aniyar kasashen ta samar da kyakkaywan yanayin kasuwanci da zuba jari. Zan iya cewa, an shafe lokaci mai tsawo tun lokacin mulkin tsohon shugaban Amurka Donald Trump, ake ta jayayya game da batutuwan da suka shafi yanayin cinikayya tsakanin manyan kasashen biyu, lamarin da bai haifar da komai ba sai koma baya har zuwa yanzu. Bangaren Amurka ya ci gaba da kakaba takunkumai da aiwatar da manufofi masu dakile ci gaban cinikayya tsakanin bangarorin biyu. Amma idan har a wannan karon Amurka za ta gyara kuskurenta, tare da samar da muhalli mai kyau na kasuwanci, to ba kasar Sin kadai ba, Amurkar da kamfanoninta za su amfana. Kyautata muhallin kasuwanci tsakaninsu zai bunkasa tattalin arzikinsu da samar da karin guraben ayyukan yi da tarin damarmakin hadin gwiwa da na ci gaba, har ma da more sabbin ci gaban kasar Sin, la’akari da yadda Sin din ta dade tana kira da kyautata huldar kasashen biyu domin moriyar juna. Haka kuma har kullum tana bude kofa tare da maraba da kamfanonin kasashen waje domin a samu ci gaba tare a duniya.
- Xi Ya Amsa Wasikar Da Tawagar Jami’an ‘Yan Sandan Kwantar Da Tarzoma Suka Aike Masa
- Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Asusun Merieux Na Kasar Faransa
Haka kuma sun amince da tabbatar da daidaito a tsakaninsu yayin da suke hadin gwiwa. Hadin gwiwar moriyar juna ba zai yuwu ba muddun wata kasa tana ganin ta fi wata. Haka kuma, ba za a taba samun kyautatuwar hulda ba muddun wata na son samun riba daga faduwar wata. Duk wata ‘yantacciyar kasa na bukatar a girmama dokoki da muradunta ko da kuwa karama ce. Idan ana son kyautata hulda tsakanin kasashen biyu, to ya zama wajibi kowacce ta girmama dayan. Kuma tabbatar da daidaito ya shafi kyale kowacce ta zabarwa kanta abun da ya fi dacewa da ita ba tare da suka ko shafa mata bakin fenti ba. Har ila yau, ya na nufin babu tsoma baki ko katsalandan game da yadda kowacce kasa ta zabi tafiyar da harkokinta na cikin gida. Don haka, kamata ya yi Amurka ta nuna da gaske take, ta girmama zabin kasar Sin da yadda take gudanar da harkokinta na gida, domin ita ta fi sanin abun da ya dace da ita da al’ummarta.
Wani batu kuma shi ne tsaro. Tsaron kasa babban batu ne ga kowacce kasa, sai dai bai kamata a rika fakewa da ita wajen dakilewa ko hana ci gaban wata kasa ba. Ya kamata duk wani zargin barazana ga tsaron kasa ya kasance bisa tushe na gaskiya da kuma adalci. Bai kamata wannan batu ya rika zama makamin tada fitina ko takala ba.
A jawabin da Janet Yellen ta gabatar ga manema labarai, ta jaddada cewa kasarta ba ta da niyyar raba gari da Sin, tana mai kiran Sin din a matsayin babbar kasuwa ga hajoji da hidimomin Amurka, tana mai cewa tattalin arzikin kasashen biyu na hade da juna. Zancenta haka yake, sai dai abun jira a gani shi ne ko a wannan karon, za a ga irin wannan furuci a aikace. Lokaci ya yi da ya kamata Amurka ta rika aiwatar da abun da take fada maimakon fadin wani abu daban, sannan ta aikata wani abu na daban.