Dan wasa Rodri za a iya cewa shi ne jigon nasarar kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, a ‘yan shekarun nan tun bayan komawarsa kasar Ingila da buga wasa daga kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta kasar Spaniya.
Dan wasan na Manchester City, ya ji rauni ranar Lahadi a karawar da suka tashi 2-2 da Arsenal a Premier League duk da cewa har yanzu ba a fayyace girman raunin ba, balle a tabbatar da kwanakin da zai yi jinya da ranar da zai koma fili, amma wasu na cewar zai dauki lokaci mai tsawo.
- Gundogan Ya Amince Ya Sake Komawa Manchester City
- Babban Taron Samar Da Kayayyaki Na 2024 Ya Sa Kaimi Ga Kulla Ayyukan Hadin Gwiwa 718
Sai dai Pep Guardiola, kociyan kungiyar ta Manchester City, bai taba boyewa ba cewar da wuya a samu wanda zai maye gurbin Rodri a kungiyar daga gurbin masu buga tsakiya wanda hakan ya sa kungiyar za ta shiga halin tsaka mai wuya. Dan wasa Kalbin Philips ana ganin zai iya buga gurbin Rodri, to amma Guardiola na hangen yana da sauran gogewa, shi ya sa ya bayar da aronsa ga kungiyar kwallon kafa ta Ipswich kuma yarjejeniya ce ta kakar wasa daya.
Wasu na ganin watakila Guardiola ya sauya tsarin yadda zai ke fara wasa ta yadda zai ke samun sauki wajen fuskantar kungiyoyi ba tare da an yi masa illa ba kuma tsohon dan wasan Chelsea, Matea Kobacic zai iya buga gurbin Rodri, ba shi kadai ne zabi ba a kungiyar ba.
John Stone kan buga tsakiya amma ba ya hawa sama sosai, domin yana aikin mai tsaron baya ne, wasu lokutan yana yi daga gefen hagu, kenan ana iya saka shi a gurbin mai wasa daga tsakiya sai Ilkay Gundogan shi ma ya buga gurbin da Rodri ke yi tun kafin ya bar Manchester City zuwa Barcelona a shekarar 2023, wanda yanzu ya sake komawa City din a bana.
Haka kuma Manchester City tana amfani da Bernardo Silba ga kuma Kebin de Bruyne, wanda ke jinya, sannan akwai matashi mai shekara 19, Rico Lewis wanda Guardiola ya ce zabi ne a wajensa, wanda ya kware a buga gurbi da yawa.
Idan har Rodri ya dade yana jinya, hakika zai kawo koma baya a Manchester City a bana, amma dai Guardiola ya kwan da sanin ya zama wajibi ya dauki mataki tun kafin dare ya yi masa, har ila yau an rufe kasuwar sayar da ‘yan wasa.