A makon da ya gabata ne, mutane 6 ciki hadda yara 3 sun mutu sakamakon harin bindiga a aka kai wata makarantar firamare da ke birnin Nashville, hedkwatar jihar Tennessee ta kasar Amurka, lamarin da ya yi matukar daukar hankalin kasashen duniya, sai dai ba a jima ba da aukuwar lamarin, an kara samun hare-haren bindiga a sassa da dama na kasar, ciki har da Los Angeles da Oklahoma da kuma yankin Hollywood na jihar California, hare-haren da suka halaka a kalla mutane 7, tare da jikkata wasu da dama. Bisa kididdigar da shafin intanet na Gun Violence Archive ya bayar, an ce, tun farkon bana har zuwa yanzu yawan mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren da aka kai ta bindiga a kasar ta Amurka ya kai fiye da dubu 10, daga cikinsu kimanin 400 yara da matasa ne.
Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya taba bayyana a watan Yuni na bara cewa: “Harin bindiga ya zama muhimmin dalilin mutuwar yara a Amurka, har ma fiye da hadarin mota ko ciwon sankara”.
Yara suna samun ilmi a makaranta ne, amma ga shi makaranta ba ta da tsaro, to ta yaya za a kare yara da matasa daga harin bindiga?
Sharaharriyar marubuciyar kasar Amurka Roxane Gay ta taba wallafa wani sharhi a jaridar New York Times cewa: “Abu mafi kunya ga Amurka shi ne, ba za a raba Amurka da bindiga ba duk da ganin yawan fushi da aka nuna kan lamarin.” Sai kuma masanin Amurka Charles Wright Mills ya taba wallafa wani littafi mai taken “The Power Elite”, inda ya bayyana cewa, Amurka wata kasa ce ba za a raba ta da masana’antun samar da makamai ba, idan wadanda suke cin moriyar masana’antun sun yi ta kare moriyarsu, to ba shakka ba za a hana yaduwar bindiga a kasar ba har abada.
To, shin ko moriyar da ake ci ta fi rayukan yara daraja? Ina “hakkin bil Adama” da ‘yan siyasar Amurka suke ta yin kirarin kiyayewa a kullum? (Mai zana da rubuta: MINA)