A ranar 18 ga watan Janairu, agogon wurin, an kaddamar da shirin bidiyo din na tallata shirin murnar bikin bazara da babban rukunin rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya tsara a cikin garin Rome, babban birnin kasar Italiya, inda aka fara share fage na ayyukan watsa labarai game da “Mu kalli shagalin murnar bikin bazara tare” na Turai.
A Burtaniya, a matsayin wani bangare na ayyukan murnar shiga sabuwar shekara ta gargajiyar kasar Sin, an nuna shirin bidiyon dake tallata shagalin murnar bikin bazara da CMG ya tsara a wurin taron manema labarai da ofishin jakadancin Sin a Burtaniya ya gudanar, wanda ya jawo hankalin jama’a daga sassa daban-daban na Burtaniya.
Mataimakin Shugaban Bankin Duniya: Tattalin Arzikin Sin Zai Kara Bunkasa A Bana
A yayin taron shekara-shekara na dandalin tattalin arzikin duniya na shekarar 2023 a birnin Davos na kasar Switzerland, shirin tallata din ya janyo hankulan wakilai mahalartan taron daga kasashe daban-daban.
Nan gaba, za a watsa shirye-shiryen musamman na bidiyo cikin harsuna da dama mai taken “Mu kalli shagalin murnar bikin bazara tare” a manyan gidajen talabijin da kafofin watsa labarai na zamani sama da 60 a kasashen Italiya, da Sfaniya, da San Marino, da Serbia, da Arewacin Macedonia, da Albania da sauran kasashen Turai, kuma ana sa ran al’ummar Turai miliyan 80 za su kalli bidiyon.
Bugu da kari, a jajibirin bikin bazara, fim din dake talla shagalin murnar bikin bazara, zai isa gidajen sinima da na wasannin motsa jiki na kasar Amurka, wanda ya kawo kyakkyawan yanayi na bikin bazara ga jama’a da dama, kuma ya zama wani kyakkyawan dandamali na baje kolin al’adun bukukuwa da na gargajiyar kasar Sin.
Jiya Alhamis ne, aka gama dukkanin atisaye sau biyar da aka tsara, don nuna shagalin kade-kade da raye-raye da sauran wasanni masu ban sha’awa na murnar shiga sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin wato shekarar zomo, da babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG zai gabatar a jajibirin sabuwar shekara, wato gobe Asabar da dare.
Shagalin zai kunshi kade-kade da raye-raye, da wasannin kwaikwayo masu ban dariya, da wasannin gargajiya, da wasan Kungfu, da wasan yara da sauransu, wadanda za’a gabatar da su bisa fasahohin zamani da dama, a kokarin nuna kasar Sin mai jajircewa da ci gaba a sabon zamanin da muke ciki, da shaida yadda al’ummar kasar ke jin dadin rayuwarsu.
Da daren ranar Asabar ne, ake sa ran galibin Sinawa dake gida da waje za su kalli shirin da CMG zai watsa kai tsaye, domin murnar shiga sabuwar shekarar gargajiyar kasar.
Sannan a ranar Juma’a, kafar CMG ta gabatar da jerin sunayen shirye-shiryen shagalin kade-kade da raye-raye da sauran wasanni masu ban sha’awa na murnar shiga sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin wato shekarar zomo.
Shagalin zai kunshi kade-kade da raye-raye, da wasannin kwaikwayo masu ban dariya, da wasannin gargajiya, da wasan Kungfu, da wasan yara da sauransu, wadanda za’a gabatar da su bisa fasahohin zamani da dama, a kokarin nuna kasar Sin mai jajircewa da ci gaba a sabon zamanin da muke ciki, da shaida yadda al’ummar kasar ke jin dadin rayuwarsu.
Da karfe 8 a daren ranar Asabar ne, CMG zai watsa shagalin kai tsaye, domin murnar shiga sabuwar shekarar gargajiyar kasar. Sannan za a watsa wasu shirye-shiryen da aka tsara su da harshen Hausa a Shirin “Kwadon Baka” na kafar Hausa ta StarTimes a Najeriya a mako mai zuwa. (Mai Fassarawa: Bilkisu Xin, Murtala Zhang, Zainab Zhang)