Gwamnatin tarayya ta ce ta kammala shirye-shiryen fara bayar da Naira 20,000 ga duk matan karkara a fadin kasar nan a kokarin shirin gwamnati na Inganta rayuwar ‘yan kasa (NSIP).
An bullo da shirin bayar da tallafin ne ga ‘yan kasa masu raunin tattalin Arziki a shekarar 2020 don Inganta rayuwarsu da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke yi a karkashin shirin fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci.
Ministar kula da jin kai da bala’o’i da ci gaban jama’a Sadiya Umar Farouq ce ta bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja yayin wani taron manema labarai da masu ruwa da tsaki kan aiwatar da tallafin ga mabukata.
Farouq ta ce an yi wannan tallafin ne domin bayar da tallafi ga mata masu fama da talauci a yankunan karkara dake kasar nan.
“Za a raba tallafin kudi na N20,000.00 ga mata da maza masu fama da talauci a fadin Jihohi 36 na tarayya da babban birnin tarayya,” inji ta.
Farouq ta roki wadanda za su ci gajiyar tallafin da su yi amfani da wannan tallafin ta hanyar zuba kudaden a kasuwanci mai dorewa don inganta rayuwarsu.