Ƙungiyar Dillalan Man Futur ta Ƙasa IPMAN ta ce, shirin Iskar Gas na CNG da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ƙiriiro da shi a cikin shekaru biyu da suka wuce, abin yabawa ne.
Shugaban ƙungiyar Alhaji Abubakar Maigandi Shettima Garima ya sanar da haka a hirarsa da manema labarai a Kaduna.
- Tinubu Ya Ƙaddamar Da Asibiti, Motocin Bas Na CNG A Kaduna
- Cire Tallafin Man Fetur: Minista Ya Yaba Wa IPMAN Don Rungumar Shirin CNG
Garima wanda kuma shi ne, Shettiman Ɗakingari ya ce, ƙara faɗaɗa samar da kayan aiwatar da shirin musamman a Arewa, ya taimaka maƙuka, wajen rage tsadar Man Fetur.
Kazalika, ya sanar da cewa, hakan zai kuma ƙara ɗaga darajar fannin samar da makamashi a ƙasar, inda ya shawarci ‘yan yankin, kar su bari a bar su a baya, wajen shiga cikin shirin, domin su amafana.
Kazalika, yace shirin ya rage tsada a fannin sufuri da kara bunkasa tattalin arziki, musamman na Arewa
Garima wanda har ila yau shi ne, and Jakadan Gwandu ya yi nuni da cewa, cibiyoyin na CNG da gwamnatin taraya ta samar a jihohin Kano da Kaduna, za su taimaka wajen samar da Iskar Gas ɗin a Arewa ta tsakiya da kuma Arewa ta Gabas.
Kazalika ya ce, samar da cibiyar a jihar Sokoto wadda take kusa da Jamhuriyyar Nijar, hakan zai ƙara bunƙasa tattalin arzikin jihar
Garima ya sanar da cewa, Iskar Gas ɗin ta CNG tsafatattaciya ce kuma bata da wani tsada, inda kuma ta rage gurɓatar muhalli.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp