Shahararren Fim din Kannywood MATI A ZAZZAU wanda aka shirya a shekarar 2020 yana gab da zamowa shirin Fim na Hausa na farko da za a nuna a babbar tashar talabijin ta Netflid da ke kasar Amurka.
Jarumar Kannywood Rahama Sadau ce ta bayyana haka, inda ta tabbatar da cewar kamfanin na Netflid ya amince zai haska fim din na Mati A Zazzau a ranar 30 ga watan Disamba da muke ciki.
- CAC Ta Bayyana Dalilan Da Ke Kawo Durkushewar Kamfanoni A Nijeriya
- Rikicin Siyasar Jihar Ribas: Dattawa Da Kabilar Ijaw Sun Yi Fatali Da Sabon Sulhu Bisa Zargin Kashin Dankali
Shirin wanda hazikin mai bayar da umarni Yaseen Auwal ya jagoranta, zai zamo shiri na farko wanda aka shirya da harshen Hausa da za a nuna a babbar tashar wadda take daya daga cikin manyan tashoshin Talabijin a fadin duniya.
Rahama Sadau wadda tana daga cikin wadanda suka dauki nauyin shirya Fim din ta bayyana wannan a matsayin wani gagarumin ci gaba da harshen Hausa zai samu a idon Duniya, duba da yadda miliyoyin mutane ne ke kallon wannan tashar Talabijin ta Netflid.
Idan hakan ya faru gaskiya zai zamo babban ci gaba ga harshen Hausa da ma Hausawa baki daya, domin kuwa miliyoyin mutane ne ke kallon Netflid wanda yake daya daga cikin manyan gidajen haska fina fim da muke dasu a fadin Duniya, hakan ya sa zai zama abin alfahari ace harshen Hausa zai shiga lunguna da sako na Duniya.
Zai nuna al’adar Bahaushe kama daga yanayin suturarsa, abincin da yake ci, yanayin wajen kwananshi, kasuwancin da yake yi da sauransu in ji Rahama.