Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta fara biyan ma’aikata da sabon tsarin ƙarin albashi daga daya ga watan Afrilu, 2024.
Ministan Yada labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris ne ya bayyana haka a Abuja, lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai.
- Minista Ya Biya Tarar Naira Miliyan 585 Domin A Saki Daurarru 4,068
- Shirin NPA Na Kula Da Tashoshin Jiragen Ruwa A Dunkule Zai Bunkasa Tattalin Arzikin Cikin Teku
Idris ya ce gwamnatin tarayya za ta daina biyan naira 30,000 a matsayin mafi ƙarancin lbashi daga ƙarshen watan Mayu, 2024.
Bayan wani nazari mai zurfi da majiɓinta kula da harkokin kuɗaɗen gwamnatin tarayya suka yi, an bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya za ta kashe naira tiriliyan 24.66 a tsakanin shekarar 2024 zuwa 2026 wajen biyan albashi.
Bayan Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin fetur a ran 29 ga Mayu, 2023, sai Gwamnatin Tarayya ta bijiro da ƙarin naira 35,000 kan gundarin albashin kowane ma’aikacin, a matsayin tallafin rage raɗaɗin tsadar rayuwa na wani taƙaitaccen lokaci na watanni shida.
To sai dai kuma a lokacin, ƙungiyar ƙwadago ta tayar da ƙayar baya cewa tallafin na toliyar naira 35,000 kan albashin ma’aikata, lasa zuma a baki ne, tunda ba na dindindin ba ne.
Sai dai kuma a ranar Alhamis din da ta gabata, ƙungiyoyin ƙwadago sun bayyana cewa sun fara tattaunawa da Gwamnatin Tarayya, tare da jaddada cewa, dokar biyan haƙƙin biyan ma’aikacin Gwamnatin Tarayya ta ayyana cewa duk bayan shekaru biyar a riƙa yi wa ma’aikata ƙarin albashi.