Abokaina ‘yan Afirka da suka taba zuwa kasar Sin, su kan yi mamakin saurin bunkasuwar tattalin arziki da zaman al’umma na kasar Sin, har ma su kan tambayi mene ne sirrin hakan. Lallai, abin haka yake, a cikin shekaru sama da 70 da suka wuce, kasar Sin ta bunkasa har ta zamanto kasa mai karfin tattalin arziki ta biyu a duniya, ko da yake ta taba fuskantar koma bayan tattalin arziki a farkon kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin. A yayin da karfinta ya dada bunkasa, kasar ta kuma tabbatar da walwalar al’ummarta. Lallai tsarin shirin raya tattalin arziki da zaman al’umma na shekaru biyar biyar ya taka muhimmiyar rawa wurin samar da nasarori masu ban al’ajabi.
Tsara shirye-shirye kafin an fara wani aiki, tushe ne na cimma nasararsa, musamman wajen gudanar da harkokin mulkin kasa. Shirin raya tattalin arziki da zaman al’umma na shekaru biyar biyar jadawali ne kuma taswira ce da gwamnatin kasar Sin ta tsara don nuna alkiblar bunkasar tattalin arziki da zaman al’umma cikin duk shekaru biyar, wanda cike yake da burikan da kasar Sin ke neman cimmawa cikin gajeren lokaci. A sa’i daya kuma, ba shiri daya kawai ake samu ba, jerin shirye-shirye ne, wato bayan an kusan kammala wannan, to, za a tsara wani sabon shirin da za a aiwatar cikin sabbin shekaru biyar na gaba, don a ci gaba da dorawa kan kokarin da aka yi. Wato ke nan, tsarin shirye-shiryen shekaru biyar biyar ya hada burikan da kasar Sin ke neman cimmawa cikin gajeren lokaci da ma dogon lokaci, ya mai da burin da kasar ke neman cimmawa cikin dogon lokaci ya zama ayyukan da za a aiwatar a matakai daban daban, wadanda suka shafi fannonin siyasa da tattalin arziki da al’adu da muhalli da sauransu, tare da gabatar da matakan da ya kamata a dauka, ta yadda za a kai ga cimma burikan bisa kokarin da aka yi a matakai daban daban.
Tun daga gabatar da shirin karo na farko a shekarar 1953 zuwa yanzu, gaba daya kasar Sin ta tsara irin wadannan shirye-shiryen raya kasa na shekaru biyar biyar har 14. Idan muka waiwaya, bisa kokarin da aka yi wajen aiwatar da shirin karo na farko har zuwa na biyar, kasar Sin ta kai ga kafa cikakken tsarin masana’antu da na tattalin arziki, kuma ayyukan noma ma sun yi matukar inganta a kasar, ban da haka, kasar ta kuma samu babban ci gaba a fannonin ilimi da kimiyya da al’adu da kiwon lafiya da wasannin motsa jiki. Daga shirin karo na shida har zuwa na bakwai kuma, kasar Sin ta kai ga magance matsalar samar da abinci, kuma ta tufatar da dukkanin al’ummominta. Shirin karo na takwas da na tara kuma sun taimaka wajen ganin mizanin hada-hadar tattalin arziki na GDP kan kowane dan kasar ya ninka na shekarar 1980 har sau biyu. Sai kuma bayan da aka kammala aiwatar da shirin karo na 10 da na 11, mizanin hada-hadar tattalin arziki na GDP na kasar ya karu har zuwa matsayi na biyu a duniya. Bisa aiwatar da shirin karo na 12 da na 13, kasar Sin ta inganta nasarar da ta cimma wajen tinkarar matsalar hada-hadar kudi da ta addabi kasashe da dama, wanda hakan ya aza harsashi mai inganci ga gina zaman al’umma mai matsakaicin wadata. Sai kuma shirin karo na 14 da aka aiwatar daga shekarar 2021 zuwa bana, wanda ya bude sabon babin zamanantar da kasar Sin mai tsarin gurguzu daga dukkan fannoni.
Sinawa kan ce, bisa mataki mataki ake yin tafiya tsawo. Lallai nasarorin da kasar Sin ta cimma, sun faru ne sakamakon yadda al’ummomin kasar suka hada karfi da karfe a karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma suka yi ta yin kokari ba tare da kasala ba bisa shirye-shiryen raya kasa da gwamnati ta tsara na shekaru biyar biyar. Shirye-shiryen cike suke da burikan da kasar Sin ke neman cimmawa, wadanda kuma suka shaida kokarin da al’ummar kasar suka yi da ma wahalhalun da suka sha. Idan aka fara wani sabon shirin, to, an bude sabon babi na bunkasa kasar ke nan. Ma iya cewa, tarihin shirye-shiryen raya tattalin arziki da zaman al’umma na kasar Sin na shekaru biyar biyar, tamkar tarihin bunkasuwar kasar Sin ne.
In an yi nazari a kan tsarin shirye-shiryen raya tattalin arziki da zaman al’umma na kasar Sin na shekaru biyar biyar, to, za a fahimci yadda kasar Sin ke gudanar da harkokinta. Tsarin ya shaida mana wata hanyar zamantar da kasa da ta sha bamban da ta kasashen yammacin duniya, wanda ya samar da darasi abin koyi ga kasashen Afirka da ma sauran kasashe masu tasowa wajen gaggauta bunkasa ayyukan masana’antunsu.
A bana ne ake kammala aiwatar da shirin bunkasa tattalin arziki da zaman al’umma na shekaru biyar biyar karo na 14 a kasar Sin. Daga yau Litinin 20 ga wata har zuwa ranar Alhamis 23 ga wata, za a gudanar da cikakken zama karo na hudu na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 20, inda za a fi mai da hankali a kan tattauna shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 15, don tabbatar da taswirar raya kasar cikin shekaru biyar masu zuwa, wato daga 2026 zuwa 2030. Mene ne alkiblar bunkasar kasar Sin nan da shekaru biyar masu zuwa, kuma wadanne damammaki ne kasar za ta samar wa duniya? Ba shakka, taron zai ba mu amsa. Sai dai abin da muke da tabbaci a kai tun yanzu shi ne, kasar Sin za ta kare niyyarta ta fadada bude kofarta ga duniya, kuma za ta kare niyyarta ta samar da damammaki ga kasashen duniya, haka kuma za ta kare niyyarta ta inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya yadda ya kamata don a ci moriyar juna da kuma samun nasara tare.