Shirin sufuri na kyauta da gwamnatin Kaduna ke gudanarwa na amfani da motocin masu amfani da iskar Gas (CNG ) ya ɗauki fiye da fasinjoji miliyan 1.4 a kan manyan hanyoyi guda huɗu tsakanin watan Yuli zuwa Nuwambar 2025, Ina da ya adana wa mazauna jihar fiye da naira biliyan 1.39 na kuɗin mota. Kamar yadda rahotanni Suka ruwaito .
Yayin gabatar da bayanan ga manema labarai a Kaduna ranar Alhamis, Kwamishinan Yaɗa Labarai, Malam Ahmed Maiyaki, ya ce an gudanar da wannan tantancewar ne domin gano ainihin tasirin tsarin sufuri kyauta da Gwamna Uba Sani ya ƙaddamar, inda alkaluman suka nuna cewa amfanin jama’a ya ninka tsammanin farko.
- Binciken Ra’ayoyi Na CGTN: Sin Ta Bukaci Japan Ta Janye Katobararta
- Kyaftin Ɗin Tawagar Super Eagles Ya Yi Ritaya Daga Buga Ƙwallo A Nijeriya
Maiyaki ya ce shirin, wanda aka fara shi domin ma’aikatan gwamnati da ɗalibai, daga baya an faɗaɗa shi domin ya amfanar da dukkan jama’a masu zirga-zirga a kan layukan da aka ware. “Daga 7 ga watan Yuli zuwa ƙarshen Nuwamba, motocin sun dauki adadi mai ban sha’awa na mutanenmu ba tare da an biya komai ba,” inji shi.
Binciken ya nuna cewa a kwata ma uku n a 2025 wato daga watan Yuli, Agusta da Satumba motocin sun ɗauki fasinjoji 683,650, Kimanin kuɗin haya na waɗannan zirga-zirgar dai ya kai naira miliyan 738.8 wanda zai kasance tanadin kuɗi kai tsaye ga al’umma.
Adadin fasinjoji ya ƙaru a watanni biyu na gaba. Daga watan Oktoba zuwa Nuwamba, motocin sun ɗauki fasinjoji 626,710, daidai da kuɗin haya da aka kauce na ₦667.2 miliyan. A Watan Oktoba kaɗai ya bada fasinjoji 339,530 saboda dawowar makarantu da ƙaruwa a safarar cikin birni.
Yace “Jimillar kuɗin da jama’ar Kaduna suka tsira da shi daga waɗannan hanyoyi huɗu ya kai naira biliyan 1.39 cikin watanni biyar kacal,”
Maiyaki, ya kara da cewa alkaluman sun tabbatar da ƙudirin gwamnan wajen rage raɗaɗin tattalin arziki a kan jama’a.
Ya bayyana cewa motocin suna aiki ne a tashoshi 200 a Kaduna, Zariya da Kafanchan, tare da motocin CNG 30 da ke aiki kullum daga karfe 7:00 na safe zuwa 6:00 na yamma. Hanyoyin sun haɗa da: Tudun Wada–Kawo–Rigachikun, Rigachikun–Yakowa–Maraban Rido, Rigachikun–Kasuwa–Maraban Rido, da Rigasa–NEPA Roundabout.
A cewar Kwamishinan, adadin fasinjojin da ake ɗauka a kullum ya kai guda miliyan 18,426, wanda yayi dai dai da 294,824 a kowane wata. Ya ƙara da cewa kowace mota na yin tafiye-tafiye takwas a rana, abin da ke nuna babban buƙata da karfin aiki.














