A ranar 23 ga Janairun 2025, za mu kaddamar da Shirin Bukatun Jama’a (HNRP) na 2025. Shirin ya shafi mutane miliyan 3.6 daga cikin wadanda suka fi fama da rauni a jihohin Borno, Adamawa da Yobe (BAY), inda ake bukatar tallafin Dala miliyan 910.2.
Shirin HNRP a Nijeriya na 2025, na da nufin tallafawa wadanda kalubalen rikice-rikice ya fi shafa a kasar da ke bukatar agajin gaggawa.
- Dole Mu Bai Wa Matasan Nijeriya Dama A 2027 – Bafarawa
- NAPTIP Ta Ceto ’Yan Mata 9 Masu Juna Biyu A Abuja
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya, Muhammad Fall ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya kara da cewa, “daga abin da ya shafi yin hijira da ke haifar da rikice-rikice zuwa wani yanayi, karancin abinci, da barkewar cututtuka, Nijeriya na ci gaba da fama da matsalolin da ke dagula albarkatu da ayyukan jin kai.”
Duk da haka, wadannan kalubalen suna ba da damar sake tunani, gyara, da daidaita kokarinmu don samun ingantaccen sakamako, mai tasiri da dorewa.
Fall ya ce, “tsarin HNRP na Nijeriya a 2025 tsari ne da aka samar da nufin magance wadannan rikice-rikice masu yawa. Kimanin ‘yan Nijeriya miliyan 33 ne ke fuskantar matsalar karancin abinci, yayin da yara miliyan 1.8 ke fuskantar barazanar rashin abinci mai gina jiki, da kuma milyoyin da suka rasa matsugunansu a fadin kasar.
“Rikicin da ke faruwa a Nijeriya ya samo asali ne daga rikice-rikice da suka shafi tabarbarewar tattalin arziki da sauyin yanayi. Jihohin BAY dai na ci gaba da zama kan gaba, inda mutane miliyan 7.8 ke da da bukatar agajin gaggawa.
“A lokaci guda kuma, bala’o’i masu alaka da sauyin yanayi, irin su mummunar ambaliyar ruwa na 2024, sun lalata gidaje, filayen noma, da muhimman ababen more rayuwa.
“A karshe, shirin yana kokarin raba hanyoyin samun kudi. Hanyoyin ba da tallafi, sabbin hanyoyin da suka hada da hada hannu da kamfanoni masu zaman kansu da tsare-tsaren da gwamnati ke jagoranta, hakan na da matukar muhimmanci wajen cike gibin da ake da shi,” in ji shi