Mai bai wa shugaban kasa shawara, kuma shugaban kwamitin aiwatar da garambawul kan harkokin kiwon dabbobi, Farfesa Attahiru Jega, ya yi gargadin cewa; Nijeriya na iya fuskantar kasadar karancin abinci mai gina jiki ga yara, idan har ba a aiwatar da tsarin sake fasalin kiwon dabbobi na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.
Ya kuma bayyana cewa, a kokarin da ake yi na cike gibin da ake da shi a bangaren abinci mai gina jiki, Nijeriya na kashe makudan kudade da suka tasamma Naira biliyan 1.5 a duk shekara, wajen shigo da kayayyakin kiwo; wanda galibi madara ta fi yawa, wadda ke da kuma karancin sinadarin gina jiki.
- APC: Ko Sadaukarwar Ganduje Za Ta Dakile Barazanar Jam’iyyun Adawa A Zaben 2027?
- Lardin Hainan Na Kasar Sin Ya Samu Karuwar Cinikayyar Hajoji Da Aka Daukewa Haraji Cikin Shekaru Biyar
Haka zalika, Jega ya ce; “Daga nan zuwa shekarar 2030, idan ya kasance an aiwatar da tsare-tsare da kuma gyare-gyare a kan kiwon dabbobi na shirin Shugaba Tinubu, Nijeriya za ta samu nasarar kirkiro ayyukan yi kusan kimanin miliyan biyar ga matasa, ta fuskar samar da wadataccen nama, kiwo, fata da sauran kayayyakin da kamfanoni ke bukata, musamman don taimaka wa matasa da mata a yankunan karkara da birane, wajen samun ayyukan yi.”
Wannan dai na zuwa ne, daidai lokacin da shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da ayyukan noma da raya karkara, Saliu Mustapha, ya ba da shawarar ware kashi 6 cikin 7 na kasafin kudin Nijeriya, domin samar da ayyukan yi a kasar.
An gudanar da laccar wannan shekara ta 2025 ne kamar yadda aka saba yi a kowace shekara, ranar Litinin da ta gabata a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara, don girmama wani dan majalisa.
Taken laccar ita ce, “Tsarin Tattalin Arziki Kan Kiwon Dabbobi A Nijeriya: Kalubale da Nasarori.”
Jega a cikin takardarsa, ya bayyana cewa; “Hasashen da aka yi, ya nuna cewa; nan da shekara ta 2050, al’ummar Nijeriya za ta karu da kusan mutum miliyan 400, wanda hakan zai sanya ta zama kasa ta uku mafi yawan al’umma a duniya. Wannan karuwar yawan jama’a, zai tilasta sake habaka bukatar naman kaji da kashi 253 cikin 100, naman saniya da kashi 117 cikin 100, sai kuma madara da kashi 577 cikin 100, domin biyan bukatun gida.
“Wadannan alkaluma, ba zato ba ne; abubuwa ne da ke kan hanya. Don haka, idan ba a yi kyakkyawan shiri da kuma zuba jari na dogon lokaci a tsarin kiwon dabbobi ba, Nijeriya na iya fuskantar matsalar karancin nama, madara, kara karancin abinci da kuma matsananciyar rayuwa, musamman a yankunan karkara,” in ji Jega.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp