Kungiyar kasa da kasa mai rajin samar da ruwa mai inganci ko IWA, ta baiwa wani shirin tsaftace ruwa na kasar Sin lambar karramawa ta kasa da kasa a fannin kirkire kirkire.
Shirin na Sin mai lakabin “Zaburar da fasaha da sauya akalar kasuwa: tsarin Sin na cin gajiya daga dabarun tace ruwa” ya yi nasarar lashe lambar girmamawa ta IWA ne a bangaren managartar kirkire kirkire na shekarar 2024, yayin taron kasa da kasa na masu ruwa da tsaki game da albarkatun ruwa, da baje kolin fasahohi da ya gudana tsakanin ranakun Lahadi zuwa Alhamis din wannan mako a birnin Toronton kasar Canada.
Kungiyar IWA ta ce aikin na samar da dabarar jure kamfar ruwa tsakanin al’ummu a matakin farko, da taimakawa ayyukan noma ta hanyar samar da kasa mai kunshe da managartan sinadarai. Kaza lika, shirin ya zama wani misali na wanzar da salon kiyaye ingancin ruwa a dukkanin fadin duniya, wanda ke iya kara zaburar da wasu karin shirye shiryen, da hadin gwiwa tsakanin abokan tafiya na kasa da kasa a fannin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp