Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), CGI Isah Jere Idris ya bayyana cewa hukumarsa ta ƙwace katin zaɓe da aƙalla katin shaidar zama ɗan ƙasa 526 daga hannun baƙi ‘yan ƙasar waje a faɗin Nijeriya.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabin buɗe wani taron da ya kira ɗaukacin manyan kwanturololin hukumar da ke sassa daban-daban na ƙasa domin shirin tunkarar ayyukan da hukumar za ta yi yayin gudanar da harkokin zaɓen 2023.
“Bisa tsarin jadawalin zaɓe na ƙasa, a yau (Laraba) jam’iyyu ke fara yaƙin neman zaɓe. A ƙoƙarin da muke yi na fara kimtsa jami’anmu manya da ƙanana domin tunkarar shirye-shiryen zaɓen da wuri, na gayyato Kwanturololin Manyan Ofisoshinmu na Jihohi domin mu ƙarfafa sintiri a iyakokin ƙasa a wannan lokacin. Ana sa ran su yi haɗin gwiwa da sauran hukumomi wajen hana kwararowar baƙin-haure da bazuwar ƙananan makamai wanda ka iya kawo cikas ga gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali da lumana.
“Bugu da ƙari za mu ruɓanya ƙoƙarinmu wajen gudanar da sintiri da sanya idanu sosai a duk faɗin ƙasar nan. Za mu yi haka ne domin tabbatar da cewa babu wani ɗan ƙasar waje da aka bari ya yi ya kaɗa ƙuri’a a zaɓen ko kuma ya haddasa fitina a wannan lokacin mai muhimmanci.” In ji shi.
Isah Jere ya ce hukumar ta duƙufa ka’in da na’in wajen tabbatar da cewa babu wani baƙo da aka bari ya yi katsalandan a zaɓen na 2023.
“Tuni muka ƙwace katinan zaɓe da na shaidar zama ɗan ƙasa na NIMC. Daga bayanan da muke da su a yau, akwai katin ɗan ƙasa 526 da muka ƙwace daga ‘yan ƙasashen waje waɗanda suka mallaka ta haramtattun hanyoyi. Nan da ‘yan kwanaki masu zuwa, muna sa ran ƙwace ƙarin wasu a sassa daban-daban na ofisoshinmu da ke ƙasar nan.”
Wakazalika, shugaban hukumar ta NIS ya gargaɗi dukkan manyan jami’an da ke shugabantar sassan hukumar kar su kuskura su bari a haɗa baki da su don mara wa wata jam’iyya baya, yana mai cewa duk wanda aka kama da laifin hakan zai ɗanɗana kuɗarsa.
“Akwai buƙatar kwanturololi na jihohi su ƙara zage damtse a wannan lokacin wajen gudanar da ayyukansu, domin duk wani abu da aka aikata da ya saɓa wa ƙa’idar aiki akwai hukunci a kai daidai da yadda dokar aikin gwamnati ta tanada.”
Har ila yau, CGI Jere ya nemi haɗin kan ‘yan jarida wajen samun nasarar ayyukan da suke gudanarwa, domin a cewarsa, “`yan jarida kuna daga cikin masu ruwa da tsaki. Labarun da kuke tattarowa yayin gudanar da ayyukanku za su iya taimakawa gaya wajen magance matsalolin tsaron ƙasa.
“Mu a NIS, mun yi ammanar cewa haɗin gwiwa da dukkan masu ruwa da tsaki yana da matuƙar muhimmanci wajen samun nasarar ayyukanmu. A kan haka, muna maraba da duk wani abu na kishin ƙasa da za a haɗa hannu da mu a kai domin tabbatar da ci gaban ƙasar da muke fatan gani a Nijeriya.
“Ina tabbatar muku da cewa a kullum ƙofarmu a buɗe take wajen karɓar bayanai da za su taimake mu gudanar da aiki tuƙuru ga ƙasa, sannan ina kira gare ku a koyaushe ku riƙa gudanar da sahihin bincike a kan duk wani labari da kuka ji a game da mu. Wannan roƙo ne na neman adalci da muke muku saboda bai saɓa wa ƙa’idar aikin jarida ba wadda ta jaddada buƙatar yi wa kowane ɓangare adalci wajen tuntuɓa don a ji ta bakinsa. A madadin mahukuntan NIS da ɗaukacin jami’anta, muna godiya da kuka amsa gayyatarmu.” Ya bayyana.
Da suke tofa albarkacin bakinsu daban-daban, Kwanturolan NIS na Jihar Bayelsa, CI Sunday James da takwaransa na iyakar ƙasa ta Jibiya, CI Kelechi Ekeoba da kuma ta Filin Jiragen Sama na Murtala Mohammed da ke Legas, CI Adeola Adeshoken, sun bayyana cewa za su miƙe tsaye domin cika aikin umarnin da CGI Isah Jere ya ba su a game da shirin hukumar na tunkarar zaɓen 2023 da sauran laifuka da suka shafi shige da fice.