Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da kara kudin da ake biya na dakon man fetur don a rage wahalhalun da motocin dako suke fuskanta wajen rarraba albarkatun man a fadin tarayyar kasar nan.
Wannan karin ya fara ne tun daga ranar 1 ga watan Yuni, amma kuma karin kudin dakon ba zai shafi kudin da ake sayar da man ba na Naira 165.00 kan lita guda.
- Ganduje Ya Jinjina Wa Buhari Bisa Tabbatar Da Dimokuradiyya
- Zabar Mataimaki: Buhari Ya Gana Da Gwamnonin APC Kan Fitar Da Mataimakin Tinubu
Amincewar ta samu ne bayan wata tattauanawa da ta gudana da kungiyoyin masu ruwa da tsaki a harkar albarkatun man fetur a Nijeriya.
A sanarwar da hukumar ta rabawa manema labarai ta bayyana cewa, yin haka ya zaman dole saboda yadda tsadar man dizal ke shafar sufurin man fetur a fadin tarayyar kasar nan.
Kan wannan dalilin yasa aka ba shugaban kasa wannan shawarar don a fuskanci hakikanin halin da ake ciki a yanzu.
“Mun yi imanin cewa, wannan karin zai karfafi kungiyar masu motocin dakon mai na kasa (NARTO) da sauran masu ruwa da tsaki wajen kara yawan motocin da suke zirga-zirgan dakon mai don tabbatar da mai ya isa lungunan kasar nan,” in ji takardar sanarwar.