Shugaban kasa Muhamadu Buhari ya amince da siyo motocin yaki masu sulke 400 ga dakarun soji, domin kare babban birnin Abuja da jihar Nasarawa da wasu yankuna na jihar Neja.
Sabon babban kwamandan rundunar soji mai lura da yankin Manjo Janar Mohammed Usman ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a cikin jawabin godiya da ya gabatar jim kadan bayan karim mukami da ya samu daga shugaba Buhari.
Manjo Janar Usman ya gode wa shugaba Buhari sabida jajircewarsa da taimakon da ya ke bai wa rundunar, ciki har da amincewa da sayo motocin sulken 400, wadanda ya ce tuni sun isa babban birnin Abuja da jihar Nasarawa da kuma wasu yankunan jihar Neja.
Haka kuma ya bayyana jin dadinsa game da karin girman da aka yi masa, yana mai cewa hakan zai taimaka masa wajen gudanar da aikinsa. Inji BBC Hausa
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp