Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya karrama Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa (NIS), CGI Isah Jere Idris da lambar yabo ta ƙasa “Member of the Order of the Federal Republic (MFR)” a yau 11 ga Oktobar 2022, a Babbar Cibiyar Taro ta Duniya da ke Abuja.
An karrama shi da lambar yabon ne bisa la’akari da yadda yake mutunta ɗan’adam a tsarin shugabancinsa da kuma namijin ƙoƙarin da yake yi wajen haɓaka ayyukan NIS a matsayin ɗaya daga cikin hukumomin kula da shige da fice na duniya mafi ƙwazo da iya aiki musamman ta fuskar kula da kai-komo da tsaron iyakokin ƙasa.
Sanarwar da Jami’in hulɗa da jama’a na NIS, Amos Okpu ya fitar ga manema labarai ta bayyana cewa, har ila yau Babban Mataimakin Kwanturola Janar mai kula da sashen bayar da biza da takardun zaman baƙi a cikin ƙasa, DCG Isiaka Abdulmumuni Haliru shi ma ya samu lambar yabon ta MFR daga shugaban ƙasa a gagarumin bikin da ya samu halartar hamshaƙan mutane.
Bikin bayar da lambar yabon dai ya kasance abin alfahari ga NIS saboda baya ga Kwanturola Janar na yanzu da ɗaya daga cikin manyan mataimakansa da suka samu lambar yabon, har ila yau akwai tsofaffin shugabanninta, Martins Kure Abeshi da Muhammad Babandede da su ma aka karrama su.
An bai wa Abeshi lambar MFR, shi kuma Babandede aka ba shi OFR. Wakazalika, akwai tsohuwar mataimakiyar Kwanturola Janar, DCG Anthonia Ifeoma Opara mai ritaya da ita ma aka karrama da lambar MFR.
Sanarwar ta ce shugabanni da sauran jami’an NIS na taya Kwanturola Janar Isah Jere Idris da sauran waɗanda aka karrama murnar lambobin yabo na ƙasa da suka samu, tare da yi musu fatan ƙarin ƙoshin lafiya da gudunmawa wajen gina ƙasa.