A ranar Talata, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar gani da ido kan aikin hako mai na farko a rijiyoyin man fetur dake jihohin Bauchi da Gombe.
Bikin kaddamar da aikin a Kolmani mai lamba 809 da 810 a filin Kolmani zai kasance aikin hako mai na farko a Arewacin Nijeriya.
An gano man fetur din ne a yankin kimanin shekaru biyu da suka gabata.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, karamin ministan man fetur na kasa Timipre Sylva, ya ce ”za a gudanar da bikin fara tono man fetur na jihohin Bauchi da Gombe a ranar Talata 22 ga watan Nuwamba Inda shugaba Buhari da wasu daga cikin ministocinsa za su halarta”
A shekarar 2016 ne kamfanin mai na kasa NNPC ya kaddamar da aikin binciko man fetur a arewacin Nijeriya, lamarin da ya kai ga gano dimbim albarkatun man fetur din a jihohin Bauchi da Gombe da Borno da kuma jihar Neja.