Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi kira ga Sin da Rasha da su ci gaba da inganta muhimmiyar dangantakar dake tsakaninsu yayin da duniya ke cikin hargitsi.
Vladimir Putin ya yi wannan kira ne jiya Talata, yayin ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a fadar Kremlin.
Yayin ganawar, Putin ya ce dangantakar Sin da Rasha na ci gaba da habaka a kan babban mataki, inda hadin gwiwarsu ke kara zurfi a fannoni da dama, kuma shekarar da ake ciki ta raya al’adu tsakanin Rasha da Sin, na samun karbuwa da goyon baya daga jama’a, lamarin dake karfafa ginshikin abotar dake tsakaninsu.
A nasa bangare, Wang Yi ya ce karkashin jagorancin shugabannin Sin da Rasha, dangantakar kasashen biyu ta zama mai juriya da karko bisa zurfafa aminci da dacewar manufofinsu da ci gaba da raya dangantakarsu a aikace.
A cewarsa, dangantakar ta kare ci gaban kasashen da muradunsu na bai daya a muhimman batutuwan kasa da kasa da na shiyya.
Yayin ziyararsa a Rasha, Wang Yi ya kuma gana da ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavrov, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi kasashensu, da ma na kasa da kasa. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp