Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya yi Allah-wadai da ikirarin da ake yi na cewa, “Shugaba Tinubu na adawa da Arewa”, inda ya ce, karya ne, kuma ikirarin sam bai dace ba.
Ya bayyana hakan ne a wata ziyarar ban girma da sabbin shugabannin kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) suka kai a gidan gwamnati Kaduna, inda ya bayyana ikirarin a matsayin makircin wasu kwararrun ‘yan siyasa.
- Sin Ta Kara Adadin Sabbin Guraben Ayyukan Yi Miliyan 6.98 A Rabin Farko Na Shekarar Bana
- ACF Ta Koka Da Rashin Tsaro Da Talauci A Arewa
A cewarsa, gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu tana ba gwamnatocin jihohin Arewa goyon baya irin wanda ba a saba gani ba don magance dimbin kalubalen da suke fuskanta.
Gwamnan ya ci gaba da bayyana cewa, dole ne masu ruwa da tsaki a Arewa su fada wa kansu gaskiya sannan su hada kai don samar da dabarun bai daya don magance kalubalen ci gaba, tare da tunkarar masu aikata laifuka da ke haddasa wa al’umma kuncin rayuwa.
Ya yi nuni da cewa, sabon kwamitin zartaswa na ACF ya zo a daidai lokacin da ake fama da manyan kalubale da ke fuskantar yankin Arewa.
“Muna fuskantar matsaloli masu wuya game da sha’anin tsaro da ke hana ci gaba. Masu aikata laifuka sun mamaye al’ummomin Arewa suna wargaza ci gaban da ta samu ta fuskoki da dama. Rashin ci gaban mu (Yankin Arewa) yana da ban tsoro kuma yana buƙatar kulawa cikin gaggawa ”
Ya ci gaba da bayyana cewa, a bayyane yake cewa, Arewacin Nijeriya na fuskantar barazanar wanzuwa kuma lokaci ya yi da kowa ya kamata ya tashi tsaye wajen kawar da yankin daga durkushewa.
Gwamna Uba Sani ya jaddada cewa, ya kamata ‘yan Arewacin Nijeriya su daina zargin wane ne ko wacce ce matsalar Arewa, kamata ya yi a nemo ta yadda asalin matsalar ta faro.
“Mun kasa yi wa kanmu wasu muhimman tambayoyi. Ta ina matsalar ta faro a Arewa? Su wane ne masu hannu a cikin rashin ci gaban Arewa? Me muka yi a daidaiku da jama’a don nemo hanyoyin magance kalubalen da Arewa ke fuskanta?
A cewarsa, kungiyar tuntuba ta Arewa, ACF na da babban rawar da za ta taka wajen samar da matsayar da ake bukata domin ganin an shawo kan kalubale iri-iri da ke fuskantar Arewacin Nijeriya.