Shugaba Bola Tinubu ya bukaci ‘yan kasar da su soke zanga-zangar ‘EndBadGovernance’ da aka shirya gudanarwa a farkon watan Agusta.
Ministan yada labaran Najeriya Mohammed Idris ne ya yi wannan kiran bayan ganawar da ya yi da shugaban kasar a fadar gwamnati dake Abuja.
- Za Mu Bankado Masu Yi Wa Nijeriya Zagon Kasa — Majalisa
- ACF Ta Koka Da Rashin Tsaro Da Talauci A Arewa
Minista Idris ya isar da sakon Shugaba Tinubu, inda ya nemi wadanda suka shirya zanga-zangar da su dakata, su bar gwamnati ta magance koke-kokensu.
“Shugaban kasa bai ga bukatar gudanar da zanga-zangar ba a wannan lokaci, ya bukaci kowa da kowa ya yi hakuri ya jira matakin gwamnati kan duk wata damuwa da ke damun ‘yan Nijeriya,” in ji Minista Idris.
Shugaban ya tabbatar da cewa yana sane da matsalolin da matasa ke fuskanta, kuma yana kokarin magance su domin ci gabansu da samu yanayi mai kyau.
Zanga-zangar da aka shirya, wadda ta yi kaurin suna a shafukan sada zumunta, ta janyo cece-kuce a fadin kasar.
Yayin da wasu ‘yan kasar ke goyon bayan zanga-zangar, wasu kuma na ganin ya kamata ayi taka-tsan-tsan game da zanga-zangar.
Rahotanni sun nuna cewa hukumomin tsaro sun fara tsare mutanen da ake zargi da hannu wajen shirya Zanga-zangar.