Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya jajantawa al’ummar Masarautar Ningi da gwamnatin jihar Bauchi, bisa rasuwar Sarkin Ningi mai daraja ta ɗaya, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya, wanda Allah ya yi wa rasuwa da safiyar Lahadi.
Shugaba Tinubu cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya fitar, ya bayyana marigayin a matsayin haziƙin shugaba da ya yi amfani da iko da dukiyar sarautarsa wajen yi wa al’umma bauta.
- Tsaro: Gwamnatin Tinubu Ta Kashe Naira Tiriliyan 3.2 A Shekara Daya
- Jawabin Tinubu Kan Kisan Sarkin Gatawa Ya Bar Baya Da Ƙura
Shugaban ƙasar ya yi addu’ar Allah ya jiƙan marigayin, tare da kuma jajantawa iyalansa da ɗaukanin al’ummar da ke jimami da alhinin rashin basaraken
Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya, ya rasu yana da shekaru 88 a duniya, inda ya shafe sama da shekaru 40 yana mulkar Masarautar ta Ningi.
An gudanar da jana’izar marigayin da yammacin yau Lahadi, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.