Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yafe wa Maryam Sanda, wadda aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello.
Maryam tana cikin mutane 175 da shugaban ƙasa, ya yi wa afuwa a taron Majalisar Ƙoli da aka gudanar a ranar Alhamis da ta gabata.
- Wakiliyar CMG Ta Zanta Da Farfesa Jeffrey Sachs Na Jami’ar Columbia
- Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 9, Sun Ƙwato Naira Miliyan 5 A Borno
A cewar mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, an yafe mata ne saboda kyakkyawar halayya da nadamar da ta nuna a cikin shekaru shida da ta kwashe tana gidan yarin Suleja.
An kama Maryam Sanda a shekarar 2017 bayan da aka zarge ta da kashe mijinta, kuma bayan shari’a mai tsawo, babbar kotun tarayya da ke Abuja ta same ta da laifi, tare da yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 27 ga watan Janairun 2020.
Fadar shugaban ƙasa, ta ce iyayenta sun roƙi a yi mata afuwa saboda tana da ’ya’ya biyu da take raino, kuma bayan bincike, an tabbatar cewa ta canza halayyarta sosai ta kuma yi nadama ta gaskiya.
Baya ga Maryam Sanda, Shugaba Tinubu ya kuma yafe wa wasu mutane da dama, ciki har da Janar Mamman Vatsa, Herbert Macaulay, da Faruku Lawan, wanda tsohon ɗan majalisar tarayya ne daga Jihar Kano.