A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron ganawa da shugabannin kasashe mambobin kungiyar BRICS karon 16, a cibiyar taruka ta birnin Kazan na kasar Rasha. Inda shugaban ya dauki hoto tare da sauran shugabannin kasashe mambobin BRICS. Sa’an nan ya halarci taron takaitattun shugabannin BRICS, gami da taron gamayyar shugabannin BRICS da ya hallara dumbin jama’a mahalarta taron, bi da bi.
A wajen taron dumbin mahalarta, shugaba Xi ya gabatar da jawabi don bayyana ra’ayinsa kan makomar tsarin hadin gwiwa na BRICS, inda ya ce, yanzu haka, duniyarmu na fuskantar sauyawar yanayi, da bukatar yin zabi tsakanin wasu mabambantan manufofi. “Shin za a bar duniya cikin halin dar-dar, da rashin kwanciyar hankali? Ko za a dawo da ita kan turbar neman samun ci gaba cikin lumana? ”
- An Kaddamar Da Bikin Murnar Cika Shekaru 75 Da Kafuwar Huldar Diplomasiyya Tsakanin Sin Da Rasha a Kazan
- Gidauniya Da Gwamnatin Zamfara Sun Tallafa Wa Mata 200 Da Kajin Kiwo
Shugaba Xi ya ce ya kamata a nuna jajircewa da jan hali, da kokarin tinkarar sauyawar yanayin da ake fuskantar, don samar da ci gaba mai inganci, ta hanyar gudanar da hadin gwiwa karkashin tsarin BRICS.
Xi ya kara da cewa, kamata ya yi a samar da tsarin BRICS mai daukaka zaman lafiya, wanda zai zama mai kare tsaron bai daya a duniya. A cewarsa, dole ne a aiwatar da tunanin tsaro mai tabbatar da moriyar juna, da hadin kai, da kwanciyar hankali mai dorewa, ta haka ne za a iya samar da tsaro ga mabambantan kasashe. Ya ce kamata ya yi a tsaya kan manufofin dakile bazuwar wutar yaki, da magance tsanantar matakan soja, da daina ruruta wuta, a kokarin sasanta halin da ake ciki a rikicin Ukraine. Kaza lika, a ingiza matakan neman tsagaita bude wuta a zirin Gaza, da yin kokari ba tare da kasala ba, don neman daidaita batun Falasdinu daga dukkan fannoni, tare da nuna adalci, da wani yanayi mai dorewa.
Ban da haka, shugaba Xi ya nanata muhimmancin samar da tsarin BRICS, wanda zai kara taka muhimmiyar rawa, a fannonin kirkiro sabbin fasahohi, da neman ci gaba mai dorewa, da aiwatar da gyare-gyare a fannin kula da al’amuran kasa da kasa, da kasancewar mabambantan al’adu tare cikin lumana. (Bello Wang)