Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon murnar ranar Australia ga gwamna janar na kasar Australia David John Hurley.
A cikin sakon, shugaba Xi ya bayyana cewa, kyakkyawar huldar dake tsakanin Sin da Australia ta dace da moriyar kasashen biyu da jama’arsu da kuma yankin da suke ciki, kana ta dace da yanayin kiyaye zaman lafiya da samun bunkasuwa na duniya. Ya ce a wannan lokaci, ya kamata bangarorin biyu su sa kaimi ga raya huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni zuwa wani sabon matsayi, bisa ka’idojin girmama juna da nuna adalci da aminci da hakuri da bambance-bambance da moriyar juna. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp