Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) Xi Jinping, ya yi kira da a kara samun nasarori a cikin sabbin kirkire-kirkire a fannin tunani a jam’iyyar.
Yayin da yake jagorantar taron nazari na rukuni na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS a jiya Jumma’a, Xi ya ce dole ne a ci gaba da zurfafa fahimtar kirkire-kirkire na jam’iyyar.
Xi ya kara da cewa, bude sabbin iyakoki wajen daidaita tsarin Markisanci da yanayin kasar Sin da kuma bukatun zamani, nauyi ne mai girma na tarihi da ke wuyan ‘yan gurguzu na kasar Sin na wannan lokaci. (Yahaya)