Babban Sakataren Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya Abuja (FCDA), Malam Shehu Ahmed, ya ce hukumar babban birnin tarayya Abuja za ta rusa dukkan gine-ginen da ke kan hanyoyin ruwa a fadin babban birnin kasar nan.
Ahmed ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Ya ce wasu gine-ginen na hana ruwa gudu ta hanyar da ta dace wanda ke haddasa ambaliya da aka samu a wasu sassan birnin.
“Mutane suna ta korafin cewa mu yi gaggawar daukar matakai don ceton rayuka. Kuma wannan shi ne abin da dole ne mu yi. Ba za mu iya kawar da kai kamar ba mu ga wannan matsala da mutane suka haifar da wadanda suka karya tsarin Abuja ba.”
” Gine-ginen da ke cikin rukunin gidaje na Trademore an yi musu alama da yawa don rushewa. An yi gargadin shekara bayan shekara amma mazauna wannan yankin suka ci gaba da yin kasada da rayukansu da na wasu.
“Mun gaya wa mazauna Trademore su yi kaura. Yankin yana kan hanyar ruwa. Ambaliyar ruwa na iya zuwa a kowane lokaci. Sun san wannan amma suka yi ta zama da wannan matsalar tsawon shekaru. ”
Sakataren zartarwa hukumar, wanda shi ne shugaban kwamitin ayyuka na musamman akan rage ambaliyar ruwa, ya bayyana cewa za a rushe wani ofishin ‘yan sanda a Trademore da sauran gine-gine.
“Muna da ofishin ‘yan sanda a Trademore za a rushe tare da sauran gine-gine. Mun sanar da rundunar ‘yan sandan FCT kuma mun samar da wurin da ya dace domin gudanar da ayyukansu da kuma yaki da masu kunnan kashi.”
Sakataren zartarwa ya nuna cewa Trademore Estate ba shi da tsarin gini na FCDA da aka amince da shi kuma wuraren da ake ci gaba da samun ambaliya za a iya barin su don zaman wuraren shakatawa ba na zama ba.