A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadi a birnin Changde na lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin.
Yayin rangadin nasa, Xi ya ziyarci titin raya al’adu, da kuma wani kauye dake birnin. Ya kuma ganewa idanun sa yadda aka farfado da gajiyar yankunan tarihi da al’adu, da yadda aka kyautata lura da muhallin ruwan birnin, da shirin aikin noman bazara, da kyautata tsarin jagorancin al’umma a matakin farko.
- Shugaba Xi Jinping Ya Taya Shugaba Putin Na Kasar Rasha Murnar Lashe Zabe
- Shugaba Xi Jinping Ya Mika Ta’aziyyar Rasuwar Tsohon Shugaban Tanzania
A lokacin da yake ganewa idon sa filin noman shinkafa dake wurin, ya ce kyautata aikin gyaran filin noma gabanin shuka, na da matukar muhimmanci ga samar da yabanya mai yalwa, da isasshen abinci.
Shugaban na Sin ya kara da cewa, ya wajaba ko wane yanki da sashe ya tabbatar da nasarar manoma, ta samun isasshen kudin shiga daga hatsi, a kuma ingiza sha’awar manoma ta rungumar noman hatsi, tare da samar da kyakkyawan mafari na fadada yawan hatsin da ake nomawa, da kudin shigar manoma a duk tsawon shekara.
Kafin wannan, Xi ya ya yi rangadi a birnin Changsha, fadar mulkin lardin Hunan a jiya Litinin, inda ya ziyarci harabar jami’ar horar da malamai ta farko ta Hunan da ke Chengnan da kamfanin batir na BASF Shanshan. Ya fahimci irin kokarin da jami’ar ke yi na kyautata yin amfani da albarkatun da suka shafi al’adun jam’iyyar, da kiyaye nagartattun dabi’u ta hanyar ilimi, da yunkurin cikin gida na hanzarta raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, da kuma fadada babban matakin bude kofa ga kasashen duniya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)