A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sako ga taron wanzar da zaman lafiya na matasan kasa da kasa, wanda a cikinsa ya ce a bana ake cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin jinin harin dakarun Japan, da yaki da masu ra’ayin danniya na duniya. Ya ce shekaru 80 da suka gabata, al’ummun Sin tare da na sauran sassan kasa da kasa, bayan aiki tukuru, da fafata yake-yake da suka haifar da zubar da jini, sun yi nasarar kakkabe ‘yan mamaya, tare da samun zaman lafiya bayan haye wahalhalu.
Shugaba Xi ya jaddada cewa, makomar zaman lafiya ta ta’allaka ga kwazon matasa. Don haka ya yi fatan matasa abokanan juna daga daukacin kasashen duniya, za su yi amfani da damar wannan taro wajen yin musayar ra’ayoyi, da bunkasa fahimtar juna tare da yaukaka abota.
Ya ce ya kamata su yayata bukatar wanzar da zaman lafiya, tare da zama jakadun bunkasa shi, kana su bayar da gudummawa, da karfin ingiza gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil’adama.
Taron na wanzar da zaman lafiya na matasan kasa da kasa na gudana ne a nan birnin Beijing a yau Talata, bisa taken “Gama kai domin zaman lafiya.” (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp