A yau Lahadi, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon ta’aziyya ga shugaban riko na kasar Koriya ta Kudu Choi Sang-mok, bisa asarar rayuka da ta faru, sakamakon hadarin jirgin saman fasinja na kamfanin Jeju Air.
Shugaba Xi ya ce ya kadu da jin asarar rayuka masu yawa da hadarin jirgin saman ya haifar. Kuma a madadin gwamnatin kasar Sin da al’ummar kasar, yana mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu, da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata. (Saminu Alhassan)