A jiya Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron liyafa na shekara-shekara na majalisar kasuwanci ta Amurka da Sin wato USCBC, inda ya mika sakon taya murna ga majalisar da dukkan mambobinta.
Xi Jinping ya bayyana cewa, dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka na daya daga cikin muhimman dangantakar dake tsakanin kasashe biyu a duniya, ba wai kawai tana da alaka da muhimman moriyar jama’ar kasashen biyu ba, har ma tana da alaka da makomar bil Adama. Hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Amurka za ta amfanar da bangarorin biyu, yayin da arangama za ta yi illa ga bangarorin biyu. Kamata ya yi mu zabi tattaunawa maimakon husuma, kuma mu aiwatar da hadin gwiwar da za ta amfanar da juna, maimakon hadin gwiwar cutar da juna. Kasar Sin a shirye take ta ci gaba da yin mu’amala da Amurka, da fadada hadin gwiwa, da gudanarwa, da sarrafa bambance-bambance, da ci gaba da bullo da hanyoyi mafi dacewa da kasashen biyu za su yi mu’amala da juna a sabon zamani, da tabbatar da zaman lafiya tsakanin Sin da Amurka cikin dogon lokaci a wannan duniyar, wadda za ta amfanar da kasashen biyu da kuma duniya baki daya. (Mohammed Yahaya)