Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya amsa wasikar hadin gwiwa da shugaban kungiyar tunawa da jarumtar tsoffin matukan jiragen saman yaki na Sin da Amurka Jeffrey Greene, da tsoffin matukan jiragen yaki na soji karkashin rundunar “Flying Tigers”, wato Harry Moyer da Mel McMullen suka aike masa.
Cikin martanin wasikar da ya rubuta, shugaba Xi ya yi fatan dorewar ruhin rundunar “Flying Tigers” zuwa zuri’o’i masu zuwa na al’ummar Sinawa da Amurkawa.
An kafa kungiyar tunawa da jarumtar tsaffin matukan jiragen saman yaki na Sin da Amurka ne a shekarar 1998, kuma kungiya ce ta kawance dake da nufin bunkasa nazari, da tunawa da tarihin abotar matuka jiragen sama na Sin da Amurka.
A baya bayan nan ne dai Jeffrey Greene, da Harry Moyer, da Mel McMullen suka rubutawa shugaba Xi wasikar hadin gwiwa, wadda a cikinta suka gabatar da goyon bayan ga tushe, da ayyukan da dakarun “Flying Tigers” suka gudanar, a fannin yaukaka kyayykawar musaya tsakanin Sin da Amurka, suna masu cewa, za su ci gaba da yayata ruhi mai kima na hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka. (Fa’iza Mustapha)