A yau Laraba 5 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da shugaban kasar Pakistan Asif Ali Zardari, a birnin Beijing.
A yayin ganawar tasu, shugaba Xi ya jaddada cewa, a ko da yaushe, kasar Sin tana kallon dangantakarta da Pakistan a mizanin manyan tsare-tsare, kana tana kiyaye zaman lumana da kawo ci gaba a manufofinta na sada zumunci da Pakistan, wadda ke mayar da hankali a kan dukkan al’ummar kasar ta Pakistan.
- Ɗalibin Jami’a Ya Hallaka Kansa Saboda Matsin Rayuwa A Jihar Kwara
- Mbappe Da Bellingham Ba Za Su Buga Wasan Da Real Madrid Za Ta Kara Da Leganes Ba
Shugaban ya ci gaba da cewa, kasar Sin kamar ko da yaushe, za ta ba da goyon baya ga Pakistan wajen kare ikonta na ‘yancin kai, da kiyaye yankunanta, da yaki da ta’addanci, da bin hanyar samun ci gaba da ta dace da yanayin kasar.
Haka nan ya ce, kasar Sin a shirye take ta zurfafa hadin gwiwa a aikace tare da Pakistan a fannoni daban daban, tare da gina yankin hadin gwiwar tattalin arziki da aka daukaka darajarsa a tsakanin Sin da Pakistan, da taimaka wa Pakistan wajen karfafa ginshikan samun ci gaba, da fitar da irin baiwar da take da ita ta samun ci gaba.
A nasa bangaren, shugaba Zardari ya ce, a karkashin hikimar jagoranci irin ta shugaba Xi, kasar Sin ta kara taka rawa a harkokin kasa da kasa, kuma tana kara zama wata muhimmin bangaren kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali da tabbatar da wadata a duniya. Don haka, Pakistan na son yin hadin gwiwa tare da kasar Sin wajen tabbatar da amfani da ra’ayoyin bangarori daban daban na duniya, da kiyaye ciniki cikin ‘yanci, da kara matsa kaimi ga cin moriyar kasashen biyu, da kuma sauran dimbin kasashe masu tasowa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp