Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, duk yadda duniya za ta sauya, Sin ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen aiwatar da manufofin kyautata yanayi, kana ba za ta sassauta goyon bayan ta ga hadin gwiwar kasa da kasa ba, kuma ba za ta yi watsi da kokarin gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil adama ba.
Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a jiya Laraba, yayin da yake jawabi ta kafar bidiyo ga taron shugabanni, dangane da kare yanayi, da sauya alkibla zuwa managartan manufofi. Ya ce a bana ake cika shekaru 10 da amincewa da yarjejeniyar Paris ta sauyin yanayi, kuma ake cika shekaru 80 da kafuwar MDD. Yayin da duniya ke fuskantar sauye-sauye cikin gaggawa irin wadanda ba a taba ganinsu a karni guda ba, al’ummar duniya na fuskantar babban kalubale.
- Tallafa Wa Al’umma: Ya Dace Gwamnoni Su Yi Koyi Da Jihar Zamfara – UNDP
- Gwamnatin Kano Ta Soke Tsaftar Muhalli A Watan Afrilu Saboda Jarabawar JAMB
Shugaban na Sin ya ce duk da cewa wasu daidaikun kasashe na kokarin aiwatar da matakan ware kai da kariyar cinikayya, wanda hakan ke haifar da mummunan tasiri ga tsare-tsaren cudanyar kasashen duniya, da dokokin da ake aiki da su, a daya hannun duniya za ta ci gaba da wanzuwa bisa mabanbantan sauye-sauye.
Ya ce, “Muddin muna da kwarin gwiwa, da karfin goyon bayan juna da hadin kai, za mu kai ga kawar da manufofi masu illa, da wanzar da daidaito da ci gaba a manufofin jagoranci a fannin kare yanayi da samar da ci gaba. ” (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp