Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada bukatar kara azamar inganta da’a a harkokin jam’iyya, da dorewa bisa turbar aiwatar da ka’idojin gudanar da kudurorin nan takwas, na shugabancin jam’iyyar kwaminis game da inganta da’a a harkokin jam’iyyar.
Xi Jinping, wanda kuma shi ne shugaban hukumar gudanarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi tsokacin ne cikin wani umarni da ya bayar, ga wani taron tattaunawa don kara gina jam’iyyar kwaminis a yau Jumma’a a nan birnin Beijing. (Saminu Alhassan)