Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon ta’aziyyar rasuwar tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter ga takwaransa na Amurka Joe Biden, yana mai bayyana marigayi Carter a matsayin wanda ya yayata manufofi da aiwatar da matakai a fannin bunkasa alakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu. Ya ce tsohon shugaban na Amurka ya shafe tsawon lokaci yana ba da gudummawa ga bunkasa alakar sassan biyu, da kyautata musayar abota da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
Shugaba Xi ya kara da cewa, alakar Sin da Amurka na cikin mafiya muhimmanci a duniya. Kuma Sin a shirye take ta hada hannu da Amurka, tare da dora muhimmanci ga moriyar al’ummun sassan biyu, da kokarin cimma nasarar burikan sassan kasa da kasa, da ingiza ci gaban dangantakarsu bisa sahihanci, da daidaito kan turba ta gari. (Saminu Alhassan)














