• English
  • Business News
Wednesday, May 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugaba Xi Ya Wallafa Makalar Da Ya Sanyawa Hannu A Jaridar Kasar Serbia

by CGTN Hausa
1 year ago
in Daga Birnin Sin
0
Shugaba Xi Ya Wallafa Makalar Da Ya Sanyawa Hannu A Jaridar Kasar Serbia
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

Sarkin Yawa Ya Fi Sarkin Karfi

Xi Ya Jaddada Kwarin Gwiwa Kan Ci Gaba Mai Inganci A Kasar Yayin Ziyararsa A Henan 

A ci gaba da ziyarar aiki da yake yi a wasu kasashen Turai, a yau Talata 7 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya wallafa makalar da ya sanyawa hannu a jaridar Politika ta kasar ta Serbia a jajibirin ya kai ziyararsa ta aiki a Belgrade.

Makalar ta shugaba Xi mai taken “Fatan hasken managarcin kawancen mu zai haskaka tafarkin hadin gwiwar Sin da Serbia”, ta hakaito shugaban na Sin na bayyana cewa, wannan ne karo na biyu da zai kai ziyara a Serbia, kasa mai kyakkyawan muhalli da dogon tarihi, tun bayan da ya kama aiki a matsayin shugaban jamhuriyar jama’ar kasar Sin.

  • Xi Ya Yi Tsokaci Kan Hargitsin Palastinu Da Isra’ila Da Rikicin Ukraine

Ya ce duk da nisan dake tsakanin Sin da Serbia, kawancen dake tsakanin kasashen biyu na kara karfafa a tsawon lokaci, wanda hakan ya samar da wani kyakkyawan misali na musaya tsakanin kasashen da al’ummunsu. Kaza lika ya jaddada cewa, ta hanyar wannan ziyara, yana fatan yin aiki tare da bangaren Serbia, wajen ci gaba da yaukaka managarcin kawance tsakanin Sin da Serbia, da aiwatar da kyawawan matakai da za su amfani al’ummun sassan biyu, da ingiza zaman lafiya da ci gaban duniya, da hada gwiwa wajen gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama.

Shugaba Xi Jinping ya kara da cewa “Bai kamata mu manta da yadda shekaru 25 da suka gabata, dakarun tawagar NATO suka jefa bam a ofishin jakadancin Sin dake Yugoslavia ba. Al’ummun Sin na martaba zaman lafiya, amma ba za su bari mummunan abu da ya faru a tarihi ya sake maimaituwa ba. Kawance na jini da tsoka tsakanin Sinawa da al’ummar Serbia, ya zamo abu da a kullum sassan biyu ke tunawa da shi, wanda kuma zai ingiza sassan biyu wajen tunkarar ci gaban su tare. A shirye muke mu yi aiki tare da abokanmu na Serbia, wajen nacewa burikan mu na asali bisa gaskiya, kana za mu ci gaba tare, za mu bude sabon babin bunkasawa, da kara farfado da kasashen mu, da gina al’ummar Sin da Serbia mai makomar bai daya a sabon zamani. (Mai Fassarawa: Saminu Alhassan).

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: SerbiaXi JinpingZiyarar Aiki
ShareTweetSendShare
Previous Post

Irin Hikima Da Karfin Da Suka Ba Da Muhimmin Tasiri

Next Post

Matashiya Ta Kashe Kanta Ta Hanyar Shan Maganin Ƙwari A Delta

Related

Sarkin Yawa Ya Fi Sarkin Karfi
Daga Birnin Sin

Sarkin Yawa Ya Fi Sarkin Karfi

5 hours ago
Xi Ya Jaddada Kwarin Gwiwa Kan Ci Gaba Mai Inganci A Kasar Yayin Ziyararsa A Henan 
Daga Birnin Sin

Xi Ya Jaddada Kwarin Gwiwa Kan Ci Gaba Mai Inganci A Kasar Yayin Ziyararsa A Henan 

18 hours ago
Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Dandalin SCO Na 2025
Daga Birnin Sin

Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Dandalin SCO Na 2025

21 hours ago
Shugaban Kasar Colombia: Ayyukan Kasar Sin Sun Nuna Wani Sabon Salo Na Ci Gaban Zamantakewar Al’ummar Bil’adama
Daga Birnin Sin

Shugaban Kasar Colombia: Ayyukan Kasar Sin Sun Nuna Wani Sabon Salo Na Ci Gaban Zamantakewar Al’ummar Bil’adama

1 day ago
Xi Jinping Ya Ziyarci Birnin Luoyang Na Lardin Henan
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Ziyarci Birnin Luoyang Na Lardin Henan

1 day ago
Kasar Sin Na Adawa Da Kai Wa Fararen Hula Da Kayayyakin More Rayuwa Hari A Sudan
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Na Adawa Da Kai Wa Fararen Hula Da Kayayyakin More Rayuwa Hari A Sudan

2 days ago
Next Post
Matashiya Ta Kashe Kanta Ta Hanyar Shan Maganin Ƙwari A Delta

Matashiya Ta Kashe Kanta Ta Hanyar Shan Maganin Ƙwari A Delta

LABARAI MASU NASABA

Hajjin Bana: Jihar Filato Ta Ba Da Kyautar Kujera 500 Da Tallafin Miliyan 2 Ga Duk Maniyyaci

Hajji: NAHCON Ta Kammala Jigilar Kashi 77 Na Mahajjatan Nijeriya Zuwa Saudiyya 

May 21, 2025
Dan Sanda Ya Kashe Abokin Aikinsa Da Almakashi Har Lahira A Kebbi

‘Yansanda Sun Kama Matasa 2 Da Ake Zargi Da Satar Mota A Kebbi

May 21, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Na Ƙara Farfaɗowa – Gwamnan CBN

Tattalin Arziƙin Nijeriya Na Ƙara Farfaɗowa – Gwamnan CBN

May 21, 2025
Gwamnan Filato Ya Kafa Kwamiti Don Binciken Hare-Haren Da Ake Kai Wa A Jihar

Gwamnan Filato Ya Kafa Kwamiti Don Binciken Hare-Haren Da Ake Kai Wa A Jihar

May 21, 2025
Sarkin Yawa Ya Fi Sarkin Karfi

Sarkin Yawa Ya Fi Sarkin Karfi

May 21, 2025
Wani Mutum Ya Kashe Matarsa Da Duka Har Lahira A Edo

Wani Mutum Ya Kashe Matarsa Da Duka Har Lahira A Edo

May 21, 2025
Na Kwana A Marte Ne Don Ƙarfafa Gwiwar Jama’a Bayan Harin Boko Haram – Zulum

Na Kwana A Marte Ne Don Ƙarfafa Gwiwar Jama’a Bayan Harin Boko Haram – Zulum

May 21, 2025
Gwamnatin Kano Ta Hana Tallace-tallacen Magungunan Gargajiya A Fina-finai Da Kan Tituna

Gwamnatin Kano Ta Hana Tallace-tallacen Magungunan Gargajiya A Fina-finai Da Kan Tituna

May 20, 2025
Xi Ya Jaddada Kwarin Gwiwa Kan Ci Gaba Mai Inganci A Kasar Yayin Ziyararsa A Henan 

Xi Ya Jaddada Kwarin Gwiwa Kan Ci Gaba Mai Inganci A Kasar Yayin Ziyararsa A Henan 

May 20, 2025
EFCC Ta Miƙa Gidaje 750 Na Emefiele Da Ta Ƙwace Ga Ministan Gidaje

EFCC Ta Miƙa Gidaje 750 Na Emefiele Da Ta Ƙwace Ga Ministan Gidaje

May 20, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.