A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da shugabar kasar Honduras Iris Xiomara Castro Sarmiento a birnin Beijing.
Yayin da yake tsokaci lokacin ganawar ta su, shugaba Xi ya ce shugaba Castro ce shugabar Honduras ta farko da ta taba kawo ziyara kasar Sin, biyowa bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasar ta da Sin a watan Maris din da ya shude.
Kaza lika shugaba Xi ya yi maraba da zuwan Castro kasar Sin, yana mai jinjinawa ziyarar aikin da take gudanarwa a Sin, wadda ya ce tana da ma’anar gaske, duba da tasirin da za ta yi wajen bude sabon babin dangantaka tsakanin Sin da Honduras.
Da yake tsokaci game da tasirin da hakan zai haifar a yanzu, da ma lokaci mai tsayi a nan gaba, shugaba Xi ya ce an bude babin cudanyar sassan biyu bisa ginshiki na gari, cikin sauri, da kuma fatan za a cimma manyan nasarori da alkawura.
Shugaban na Sin, ya kuma sha alwashin kara azamar bunkasa kawancen kasar sa da Honduras, da nacewa manufofin tallafawa tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Honduras, da fadada abota mai ma’ana, da hadin kai da Honduras bisa martaba juna, da daidaito, da cimma moriya, da kuma samun ci gaba tare.
Daga nan sai shugaba Xi ya bayyana shirin sa na yin aiki tare da shugabar Honduras a dukkanin fannoni cikin dogon lokaci, ta yadda hakan zai zaburar da alakar sassan biyu, zuwa cimma manyan nasarori, da mayar da tunanin hadin gwiwa zuwa nasarori na hakika, wadanda za su samar da manyan alherai ga al’ummun kasashen biyu. (Saminu Alhassan)