An buga mujalladi na hudu na littafin “Xi Jinping: Mulkin kasar Sin” a cikin harsunan Faransanci, Rashanci, Larabci, Sipaniya, Fotigal, Jamusanci, Jafananci da Sinanci na gargajiya, a cewar wata sanarwa da mawallafin ya fitar a jiya Lahadi.
Sabon kundin da aka buga ya ƙunshi tarin maganganu da rubuce-rubuce 109 na shugaba Xi, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, daga ranar 3 ga watan Fabrairu na shekarar 2020 zuwa ranar 10 ga watan Mayu na shekarar 2022, tare da hotuna 45 da aka dauka tun watan Janairun 2020. An raba shi zuwa babi 21 a bisa maudu’i.
Littafin ya ƙunshi tarihin manyan ayyuka na kwamitin tsakiya na jam’iyyar tare da Xi Jinping a matsayin jigo na mayar da martani game da annobar cutar COVID-19, da sauye-sauye masu tsauri, wadanda ba a taba ganin irin su cikin karni ba, da jagorantar daukacin ‘yan jam’iyyar da jama’ar kasar Sin na dukkan kabilu wajen tabbatar da manufar gina al’umma mai matsakaicin wadata daga dukkan fannoni, da fara sabuwar tafiya don gina kasar Sin a matsayin kasa mai tsarin gurguzu ta zamani daga dukkan fannoni. (Mai fassarawa: Yahaya)