Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci bikin bude taron ministoci na dandalin Sin da kasashen Latin Amurka da Karebiya ko CELAC karo na 4, kuma zai gabatar da jawabi.
An shirya gudanar da dandalin ne a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin a ranar Talata 13 ga watan Mayun nan, kamar dai yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a Lahadin nan. (Saminu Alhassan)














