Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da cewa, shugaban kasar Xi Jinping, zai gudanar da ziyarar aiki a kasar Rasha tsakanin ranakun 7 zuwa 10 ga watan nan na Mayu, bisa gayyatar da takwaransa na Rasha Vladimir Putin ya yi masa. Yayin wannan ziyara, shugaban na Sin zai kuma halarci bikin cika shekaru 80 da samun nasarar yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet, wanda zai gudana a birnin Moscow.
Rahotanni na cewa, yayin wannan ziyara, shugaba Xi zai gudanar da zuzzurfar tattaunawa tare da Putin, dangane da raya alakar Sin da Rasha karkashin sabon yanayin da ake ciki, da ma sauran manyan batutuwan kasa da kasa da na shiyyoyi. (Mai fassara: Saminu Alhassan)