Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin DIG Hashimu Argungu (Rtd) a matsayin shugaban hukumar kula da ayyukan ƴansanda (PSC). Haka kuma an naɗa Cif Onyemuche Nnamani a matsayin Sakatare da DIG Taiwo Lakanu (Rtd) a matsayin Mamba a Hukumar.
Waɗannan naɗe-naɗen na da nasaba da amincewar majalisar dattawa, tare da wasu ƙarin mambobi da za a naɗa daga baya.
- Kamfanin BUA Ya Tallafawa Asibitoci 15 A Sakkwato
- Gwamnati Za Ta Samar Da Tsaro A Filayen Hakar Ma’adanai —Alake
A wani labarin kuma, shugaban ƙasar ya amince da naɗin Mista Mohammed Sheidu a matsayin babban sakataren hukumar kula da ƴansandan Najeriya NPTF.
Waɗannan naɗe-naɗe na da nufin inganta sha’anin mulki da sa ido kan ƴansanda da asusun kuɗi lura da jin daɗinsu, tare da kudirin ƙudirin gwamnatinsa na inganta jami’an tsaro a ƙasar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp